An cutar da yaron da aka kwakule wa idanu

Assalamu alaikum Aminiya, ku ba ni dama na bayyana takaici na dangane da wani abin tausayi mai cike da rashin imani da wasu da ake zargin matsafa ne suka aikata wa wani yaron da bai ji ba, bai kuma gani ba a birnin Zariya, wato kwakule wa yaro mai kankantar shekaru ido da aka yi. […]

An cutar da yaron da aka kwakule wa idanu
An cutar da yaron da aka kwakule wa idanu

Assalamu alaikum Aminiya, ku ba ni dama na bayyana takaici na dangane da wani abin tausayi mai cike da rashin imani da wasu da ake zargin matsafa ne suka aikata wa wani yaron da bai ji ba, bai kuma gani ba a birnin Zariya, wato kwakule wa yaro mai kankantar shekaru ido da aka yi. Tabbas akwai bukatar jami’an tsaro su gudanar da bincike sahihi don gano wadanda suka aikata wannan aika-aikar, tare da ladabtar da su bisa ga Shari’a.
Kana ina kira ga iyaye mata, da su san irin wuraren da za su rika aiken ’ya’yan su, ko kuma su hada su da wadanda suka fi su wayo, domin kare afkuwar ire-iren wannan matsalar.  Hakika an kassara rayuwar wannan yaro. A daidai lokacin da muke rokon Allah Ya sa mana mafita daga musifun rayuwa, ya zama wajibi mu kula da bai wa al’umma kariya, ta yadda irin hakan ba za ta sake aukuwa ba.
A karshe ina addu’ar Allah ya saka wa wannan yaro da mafificiyar sakayya ta alheri, wadanda suka aikata wannan danyen aiki kuwa.  Allah ka hukunta su akan haka. Da fatan Allah Ya kawo mana karshen miyagun laifuka irin wannan a Najeriya, Amin.  [email protected] Usman Bin-Affan Damaturu a Jihar Yobe. 08038001563.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya