An daƙile harin ’yan ta’adda a Borno
Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta yi nasarar daƙile wani hari da ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP suka kai a ƙauyen Malari da ke Ƙaramar Hukumar Konduga. Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan, ASP Nahum Kenneth Daso ya raba wa manema labarai a yau Alhamis, ta ce tawagar da ke […]
Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta yi nasarar daƙile wani hari da ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP suka kai a ƙauyen Malari da ke Ƙaramar Hukumar Konduga.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan, ASP Nahum Kenneth Daso ya raba wa manema labarai a yau Alhamis, ta ce tawagar da ke aiki a sansanin kai ɗaukin gaggawa na ‘Forward Operating Base (FOB) da ke Malari ce ta gudanar da aikin.
- An bai wa tsofaffin ’yan bindiga 6 shaidar tuba a Yobe
- An kama matashi kan luwaɗi da yara 12 a Jigawa
A cewarsa, tawagar ‘yan sandan sun yi artabu da ‘yan ta’addan ne da misalin karfe 1:00 na tsakar dare, lamarin da ya sanya ’yan ta’addan suka tsere da raunukan harsasai daban-daban a jikinsu.
A wani bincike da jami’an tsaro suka gudanar a yankin, sun gano wani gurneti da bai tashi ba a cikin wata mota ƙirar Toyota Hilux ta ƙungiyar ’yan banga da aka yi watsi da ita.
An tura ƙwararru kan abubuwa ma su fashewa (EOD) waɗanda suka kwtare kan sunadaran haɗa bama-bamai da kuma makamantan ƙare dangi na Nukiliya (CBRN) don warware su cikin tsanaki ba tare da sun cutar da kowa ba.
Kwamishinan ‘yan sanda Mohammed Lawal Yusufu, ya yaba wa bajintar jami’an ‘yan sanda da kuma tawagar ƙwararru kan abubuwa masu fashewa bisa ƙoƙarin da suka yi cikin hanzari wajen ɗaukar matakin warware bama-baman cikin nasara.
Kwamishinan ya sake jaddada ƙoƙarin rundunar wajen tabbatar da tsaron al’ummar yankin.
Kazalika, rundunar ‘yan sandan ta buƙaci jama’a da su sanya ido tare da gaggauta kai rahoton duk wani motsi da ba su aminta da shi ba ga mahukunta mafi kusa ko kuma a tuntuɓe su ta lambobin gaggawa kamar haka: 08068075581 da 08023473293.