An dade ana yi wa Sardauna barazanar kashe shi – Babban direbansa
Alhaji Ali Sarkin Mota shi ne Babban direban Sa Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, a lokacin da yake raye, a wannan tattaunawar da ya yi da Aminiya saboda cika shekara 50 da rasuwar Sardauna, ya bayyana cewa an dade ana aika wa Sardauna takardar barazanar kashe shi, kuma su da ake wa lakabi da yaran Sardauna […]

Alhaji Ali Sarkin Mota shi ne Babban direban Sa Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, a lokacin da yake raye, a wannan tattaunawar da ya yi da Aminiya saboda cika shekara 50 da rasuwar Sardauna, ya bayyana cewa an dade ana aika wa Sardauna takardar barazanar kashe shi, kuma su da ake wa lakabi da yaran Sardauna sun zama abin kyama ga gwamnati bayan rasuwarsa, domin kuwa ko taimakonsu ba a yi. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Kana dan shekara nawa aka kashe Sa Ahmadu Bello Sardauna?
Alhaji Ali: Ina kusan dan shekaru Arba’in da wani abu dai. Ka san abin zai yi min wuyar tunawa.
Aminiya: Shekaru 50 bayan rasuwar Sardauna ya kake ji a yanzu?
Alhaji Ali: Shekaru hamsin ai kamar kwanaki hamsin ne a sha’anin ra’ayuwa, Sardauna yanzu shi yana da rai ne, amma abin da ya shuka fa? Shi ake fatan wadannan shagabannin su kwatanta, amma ba su yi ba.
Aminiya: Tun bayan kashe shi wane asara kake ganin yankin Arewa ya yi?
Alhaji Ali: Ai har gobe Arewa na cin arbarkacin Sardauna, duk abin da ya tashi za a a ce Sardauna. Ku kuma (Manema labarai) idan hakan ya taso za a ce ku nemo yaran Sardauna. Me aka kulla mana? Babu wani abu da gwamnati ta kulla mana. Har yanzu albashina na fansho bai wuce Naira dubu goma ba. Kuma Allah bai hana mu abin da za mu ci ba. Sai dai akwai wadanda ke tunawa da Sardaunan suke taimaka mana. Mun gode, sai dai Allah Ya saka masu.
Aminiya: An ce a ranar da Sardauna zai rasu ya nuna wadansu alamu, haka ne?
Alhaji Ali: Sardauna dai kowa ya san kiyayya ce ta yi sanadin kashe shi da aka yi. Ai alama ita kusan an shekara biyar duk rana ta Allah zai samu takardu talatin ko ashirin ana cewa rana kaza ga wata kaza za a zo a kashe ka. Tun ana damuwa har ya zo ba a damuwa. A ranar da aka kashe shi sojoji sun shigo sun same ni ina wanke mota da misalin karfe daya na dare, saboda za a yi bako, sai suka ce in in je in kwanta dare ya yi. A lokacin da Sardauna ya gan ni har ya ba ni kilishi ya ce in bai wa wadansu. Da sojojin suka yi ido biyu da shi, suke nemi kashe shi, sai uwargidansa Hafsat ta rungume shi, ita suka fara kashewa, sannan suka kashe Sardauna.
Aminiya: Kana ganin za a iya samu wani shugaba kamar Sardauna a yankin Arewa kuwa?
Alhaji Ali: Kai me ka gani? ai kai dan jarida ne.
Aminiya: Ba za a samu ba ke nan.
Alhaji Ali: (Dariya) amsa ke nan.
Aminiya: Ta wace hanya matasa irinmu za su yi koyi da halayen Sardauna?
Alhaji Ali: Allah Ya sa ku yi. Ai mutane biyu aka yi asara a Arewa da shi Sa Ahmadu Bello da kuma Shaikh Abubakar Gumi. Ina wadansu kamarsu?
Aminiya: Wane jan hankali za ka yi ga shugabanin Arewa wadanda suka amfana da mulkin Sardauna?
Alhaji Ali: Ai ka ga tun da sun san mun san inda suka fito don haka ba su neman su ganmu domin mun san asalinsu. Dan haka ba mu kusa da su su ma ba su kusa da mu.
Aminiya: Yanzu ke nan ku da su sai dai kowa tashi ta fishe shi ?
Alhaji Ali: Eh, amma ba duka aka taru aka zama daya ba. Akwai ‘yan halak da suka zamanto suna tare da Sardaunan dai masu taimakawa.
Aminiya: Ke nan dai kana nufin an manta daku tun bayan rasuwar Sardauna?
Alhaji Ali: kwarai kuwa, an manta da mu, ba a ko nemanmu sai idan abu ya taso irin haka a ce a nemo mutanen Sardauna. Ko gwamnati babu ruwanta da mu, domin a Yanzu mun zama abin kyama. Mu kuma babu ruwanmu . Yanzu dai mu biyu muka rage a raye daga nan har jahar Sakkwato, daga ni sai Sani One minute. Mune yaran sardauna.
Aminiya: Yanzu a Arewa wa za mu ce yana koyi da halayen Sardauna?
Alhaji Ali: Ni ba zan iya cewa ga wani ba, amma dai ku kanku kuna iya tambayar kanku.
Aminiya:Ya kusancinka yake da Sardauna?
Alhaji Ali: Ni Direbansa ne, amma kusan yadda ya dauke mu an wuce haka, sai dai akwai mataimaka, misali Sani One minute, wanda odili ne na Sardauna kuma ya iya mota, akwai kuma Malam Ali Odili, shi ma ya rasu, Sarkin Kano Sanusi ya ba Sardauna shi.
Aminiyi: Ke nan kana Unguwar Sarkin Musulmi tun lokacin da Sardauna yake raye?
Alhaji Ali: kwarai kuwa, ina nan a Unguwar nan ban je ko’ina ba. Muna da gida Zariya, amma ban je ko’ina ba. Ka san ni mutumin Zariya ne.