An dade ana yin coge a cikin kasafin kudi – Lawal Gumau
A ranar Alhamis da ta gabata ce dan Majalisar Wakilai mai wakiltar karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi Alhaji Lawal Yahaya Gumau, ya bayyana a shirin Sunrise (Gari ya waye) da ke tattauna al’amuran yau da kullum a gidan talabijin din Channels Telebision, inda a tattaunawar dan majalisar wanda wakili ne a wata kungiyar ’yan […]
A ranar Alhamis da ta gabata ce dan Majalisar Wakilai mai wakiltar karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi Alhaji Lawal Yahaya Gumau, ya bayyana a shirin Sunrise (Gari ya waye) da ke tattauna al’amuran yau da kullum a gidan talabijin din Channels Telebision, inda a tattaunawar dan majalisar wanda wakili ne a wata kungiyar ’yan majalisar mai suna Transparency Group wato kungiyar Tabbatar da Gaskiya da Rikon Amana, ya bayyana gaskiyar yadda ake yin coge a Majalisar Dokoki ta kasa kan kasafin kudin. Ya bayyana cewa wannan almundahana abu ne da ake yi duk shekara. Kuma ya yi bayani dalla-dalla kan yadda ake yi cogen ta yadda ’yan Najeriya za su yi saurin fahimta. Jaridar Premium Times ta nakalto hirar kamar haka:
Kana cewa an dade ana yin coge a cikin kasafi ba yanzu aka fara ba?
Na zo Majalisar Dokoki ta kasa ne a shekarar 2011 kuma na yi ta fada da yadda ake coge a cikin kasafi tun shekarar 2012, duk shekara sai an yi coge. Babu wanda zai ce ba a yin coge. Ya kamata mu fara bincike a kai, kuma duk wanda ya bincika zai ga ana yin wannan coge.
Mene ne hakikanin abin da ake nufi da cogen?
Coge shi ne a sanya wani abu a cikin wata takarda da niyyar ka kamsar da kanka ko ka boye wani bayani. Ka je ka duba duk wani kamus wannan ne ma’anarsa. Kafin mu fito jiya mun duba kamus-kamus daban-daban mun ga ma’anar coge. Kuma wajibi ne mu yi wa jama’a adalci.
Wato suna sanya wasu abubuwa ne domin jin dadin kawunansu?
Ga misali, za ka iya gaya min a yanayin da ’yan majalisa biyu suke zaune a nan daya yana wakiltar wata mazaba a Jihar Bauchi, dayan ma yana wakiltar wata mazaba a Jihar Bauchi. Mutum na farko ya samar wa mazabarsa aikin Naira biliyan hudu, yayin da mutum na biyu ke da aikin Naira miliyan 70. Naira biliyan hudu da Naira miliyan 70. Yaya kake jin za a sanya mutum na biyu a cikin kunci. Sannan mutum na farko bai sanar da Majalisar Dokoki ta kasa cewa yana son ya sanya Naira biliyan hudu don yin aiki a mazabarsa ba.
A bayanan da majalisa ta fitar da farko lokacin da Jibrin ya yi zarge-zargensa, sun ce suna da hanyoyinsu da shugabannin majalisa suke samun manyan kudi da ake warewa domin yin a ayyuka a mazabunsu da ake mika wa Majalisar Wakilai ko ta Dattawa, kuma wannan ne al’adar da ake yi a dogon lokaci?
Na gode kwarai da gaske. Ga dabi’a ba za yi tsammanin Janar Manajan gidan talabijin na Channels Tb ya samu abin da kake samu ba. Ga al’ada kowane shugaba kan samu abin da ya fi na mabiyinsa. To amma abin da muke fadi shi ne ana yin cogen ne bayan wancan kaso.
Misali, ayyukan da ake sanyawa na shiyya-shiyya ana rarrabawa ne a tsakanin shiyyoyin siyasa shida. Kuma a tsakanin wadannan shiyyoyi shida kowace jiha tana da kasonta. Wannan sananne ga kowa. Inda matsalar take shigowa shi ne akwai wasu bayanai da shugabannin suke boyewa wadanda ba su shaida wa sauran wakilan, su kadai suke amfani da wadannan bayanai. Shin wannan ba coge ba ne?
Ga al’ada shugaba zai samu abin da ya fi girma, amma abin da za ka ji mamaki shi ne a ce shugaba ya Naira biliyan hudu, mabiyinsa kuma ya tashi da miliyan 40. Ina da aboki a Jihar Anambra har zuwa yau Shugaban Majalisar Wakilai bai tura ko kwabo a asusunsa ba. saboda kawai dalili na kashin kai saboda dalili na son zuciya domin sun samu sabani. Ko a jiya ya zo ofishina yana shaida min babu ko kwabo a asusunsa. Na ba shi shawara ya je wurin Shugaban Majalisar Wakilai, sai ya ce ya je ya fi sau 10. Kuma ko kafin a cire Jibrin ya je ofishinsa ya fi sau biyar, amma babu abin da aka yi.
Wato hakan na nufin zauren majalisa bai ganin kwafe na karshe kafin a aike ga Majalisar Dattawa don amincewarta bayan an aike ga bangaren zartarwa, gaba dayan zauren majalisar bai ganin kwafe na karshe dag alibi mutane suke cewa sun amince da shi. Wannan shi ne yake faruwa?
Ina fata wata rana za ka kasance a majalisar ka ga yadda wadannan abubuwa suke faruwa balo-balo. Saurare ni. A bayan kasafin kudi daga kwamitoci ya isa kwamitin kasafi za su yi aiki a kasafin. Bayan sun yi aiki a kan kasafin kwamitin zai dawo da shi ga zauren majalisa wanda zai karanta shi ya samu matsaya a kai. To da zarar majalisa ta amince da shi kafin a mika shi ga Shugaban kasa ake sanya cogen, to a wannan wuri ne cogen ke shigowa.
Shugaban kasa ba zai san cewa wannan aiki ba ya cikin kasafin da wakilan majalisa suka amince da shi ba. Sai Shugaban kasa ya sanya hannun amincewa da shi. Su ma sauran ’yan majalisa ba za su san bayan sun amince da kasafi an sanya wani abu a ciki ba. Don haka abin da muke cewa shi ne, lokacin da suka dawo da kasafin da aka amince da shi (aka sanya masa hannu), to a nan ne sauran ’yan majalisa za su san an shigar da wani abu kari a kana bin da muka amince da shi.
Idan ka yi magana a kan shigar da wani abu kana magana ce a kan sabon jerin abubuwa da aka shigar ne ko a kan kudi ne aka kara?
Eh, sababbin jerin abubwa ne. Bari in ba ka misali a fili. Wannan aiki na kauyen Fina-Finai a Kano da jama’a ke muhawara a kai ba mu amince da shi ba a kasafin. An shigar da shi ne a cikin kasafin kafin a dauke shi zuwa ga Shugaban kasa don ya sanya hannu a kai da kudin da aka ware wa aikin. Ku je ku duba ayyukan mazabu na dukkan shugabannin, musamman wadanda Jibirin yake zargi, za ku sha mamaki cewa baya ga ayyukan tallafi na shiyya-shiyya da aka ba mazabunsu, sun kuma yi gaban kansu sun sanya biliyoyin Naira a mazabun nasu.