An daga darajar masarautar kauyen Shugaba Buhari
Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta yi wani zaman gaggawa duk da hutun da ’yan majalisar suke yi domin amincewa da kirkirowa da kuma daga darajar masarautar kauyen su Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zuwa matsayin kasar Hakimi a Masarautar Daura. Masarautar Hakimin da Mai Martaba Sarkin Daura Dokta Farouk Umar Farouk ya yi ita ce Hakimin […]
Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta yi wani zaman gaggawa duk da hutun da ’yan majalisar suke yi domin amincewa da kirkirowa da kuma daga darajar masarautar kauyen su Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zuwa matsayin kasar Hakimi a Masarautar Daura.
Masarautar Hakimin da Mai Martaba Sarkin Daura Dokta Farouk Umar Farouk ya yi ita ce Hakimin Dumurkul tsohon garin da yake mahaifar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
- An kama matashi da bindigogi da rigar Fulani a Kafanchan
- ‘Akwai yiwuwar kudin kiran waya da na data ya karu a Najeriya’
Kamar yadda Shugaban Kwamitin Majalisar kan Kananan Hukumomi da Masarautu, Garba Husaini Dankanjiba ya ce, kirkiro irin wadannan hakimai a masrauta yana kara bunkasa masarautar da kuma harkokin siyasar yankin.
A zaman gaggawar da majalisar ta gudanar a ranar 26 ga Yulin, bayan tafiyarta hutun Sallah a ranar 14 ga Yuli zuwa 2 ga Agusta, jagoran majalisar, Abubakar Korau ya kawo kudirin neman amincewar majalisar a kan wannan batu inda ya samu goyon bayan takwaransa Mustapha Rabe.
Rabe wanda ke wakiltar Karamar Hukumar Mai’aduwa ya ce, Gwamna Masari ne ya kawo wannan bukata wadda take a karkashin Sashi na 7 (1) da (2) na Dokar Kananan Hukumomi ta jihar ta shekarar 2000 wadda aka yi wa gyara.
Zaman majalisar wanda Shugabanta Tasi’u Musa Maigari Zango ya jagoranta, bayan tattaunawa, Shugaban ya nemi Akawun Majalisar ya tuntubi sauran ’yan majalisar don daukar mataki na gaba.
Wannan sarauta ta Hakimi ita ce ta farko da aka kirkiro a Masarautar Daura a cikin wannan shekara kuma a wannan yanki wanda a da yake karqashin Karamar Hukumar Daura, daga bisani ya koma karkashin Karamar Hukumar Mai’aduwa.