An daga zuwan Limamin Madina Najeriya

daya daga cikin manyan limaman masallacin Annabi (SAW) da ke Madinah ta kasar Saudiyya, Sheikh Salah Albudair da aka shirya zai ziyarci Najeriya na wuni uku bai samu zuwa ba a sakamakon wasu uzurori da suka bijiro. daya daga cikin wadanda suka shirya ziyarar wanda malami ne a wata jami’a a birnin Madina, Dokta Isa […]

An daga zuwan Limamin Madina Najeriya
An daga zuwan Limamin Madina Najeriya

daya daga cikin manyan limaman masallacin Annabi (SAW) da ke Madinah ta kasar Saudiyya, Sheikh Salah Albudair da aka shirya zai ziyarci Najeriya na wuni uku bai samu zuwa ba a sakamakon wasu uzurori da suka bijiro. daya daga cikin wadanda suka shirya ziyarar wanda malami ne a wata jami’a a birnin Madina, Dokta Isa Ali Pantami ya tabbatarwa Aminiya a shekaranjiya Laraba cewa limamin wanda daya ne daga cikin wadanda suka fi iya karantun Alkur’ani a duniya, an shirya zai iso Najeriya ne a shekaranjiyar sannan ya jagoranci Sallar Magariba da Isha’i a jiya Alhamis a masallacin Annur da ke Abuja, yayin da a yau Juma’a zai jagoranci Sallar Asuba da ta Juma’a a Masallacin kasa na Abuja.
Ya ce kodayake limamin matashi ne kasancewar an haife shi ne a shekara ta 1970, amma babba ne a kasar kuma daya daga cikin manyan alkalai a Babbar Kotun Madina, ya ce a yanzu an dage ziyarar zuwa wani lokaci da ba zai jima ba.