An dage dokar hana fita a Kano

Rundunar ’Yan Sandn jihar ce ta sanar da hakan

An dage dokar hana fita a Kano

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da janye dokar hana fita ta sa’o’i 24 da aka sanya da yammacin Laraba.

Kakakin rundunar a Jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook da maraicen Alhamis.

“Gwamnatin Jihar Kano ta ba da Umarnin Dage Dokar Hana Fita da Zirga-Zirga Wato “Curfew” a Jihar Kano,” kamar yadda ya wallafa.

A ranar Laraba ce Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Usaini Mohammed Gumel ya sanar da sanya dokar bayan yanke hukunci kan zaben Gwamnan Jihar.

Kotun sauraron kararrakin zabe dai ta soke nasarar da Abba Kabir Yusuf na NNPP ya samu a zaben Gwamnan jihar, inda ta ayyana Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben.

Kotun ta kuma umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ta janye takardar lashe zaben da ta ba Abba sannan ta ba Gawuna.

Zaɓen Edo: Duk wanda ya kaɗa ƙuri’a ya koma gida ya zauna — ’Yan sanda

Hotunan yadda Zaɓen Gwamnan Edo ke gudana

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo