An dage dokar kulle saboda sallar Idi a Jigawa
Jigawa ta shiga jerin jihohin da suka jingine dokar kullen coronavirus don ba da damar halartar sallar Idi. A ranar Lahadi 24 ga watan Mayun 2020 ne ake hawa Idin karamar sallar. Hukumomin jihar sun ce za a yi sallar idi har a wuraren da aka samu bullar cutar, amma ba za a yi shagulgula […]
Jigawa ta shiga jerin jihohin da suka jingine dokar kullen coronavirus don ba da damar halartar sallar Idi.
A ranar Lahadi 24 ga watan Mayun 2020 ne ake hawa Idin karamar sallar.
Hukumomin jihar sun ce za a yi sallar idi har a wuraren da aka samu bullar cutar, amma ba za a yi shagulgula ba.
A wuraren da aka sanya dokar hana fita kuma, dokar za ta ci gaba da aiki da zarar an sauko daga idi.
Gwamnatin jihar ta shawarci mata da kananan yara da tsofaffi da masu rauni da su hakura da zuwa masallatan idin.
Masallata kuma, an bukace su da su bayar da tazara a tsakaninsu kuma su sanya amawali.
Hakan na zuwa ne a sadda aka samu karuwar masu cutar a wasu kananan hukumomi takwas a fadin jihar.
Gwamna Muhammadu Badaru ya yi gargadi cewa masu cutar coronavirus a jihar na iya kaiwa 20,000 idan ba a dauki matakai ba.
Jihar ce ta fi yawan wadanda suka kamu da cutar coronavirus a Arewacin Najeriya a ranar Juma’a.
Amma alkaluman da hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa (NCDC) ta fitar ranar Asabar sun nuna ba a samu karin wanda ya kamu da cutar a jihar ba.