An dage horar da masu yin NYSC rukunin C na Kaduna
Mahukunta aikin yi wa kasa hidima wato NYSC sun sanar da dage gobe Talata 23 ga Oktoba da masu yi wa kasa hidima, rukunin C 2018 da zasu halarta a sansanin NYSC don horar da su kamar yadda aka saba. An dai dage ranar ne sakamakon kalubalen tsaron da jihar ke fuskanta. Hukumar NYSC ta […]
Mahukunta aikin yi wa kasa hidima wato NYSC sun sanar da dage gobe Talata 23 ga Oktoba da masu yi wa kasa hidima, rukunin C 2018 da zasu halarta a sansanin NYSC don horar da su kamar yadda aka saba.
An dai dage ranar ne sakamakon kalubalen tsaron da jihar ke fuskanta.
Hukumar NYSC ta sanar wadanda zasu yi hidimar kasa a jihar da su zauna a jihohinsu har sai an sanar da su lokacin da aka shirya.