An dage sauraron karar Hadiza Gabon saboda rashin lafiyar matar alkali
Za a ci gaba da shari’ar ranar 1 ga watan Agusta, 2022.
An dage sauraron karar da aka yi na jarumar fim din Kannywood, Hadiza Gabon a Kotun Shari’ar Musulunci da ke Magajin Gari a Jihar Kaduna zuwa ranar 1 ga watan Augusta.
A kwanakin baya ne wani ma’aikacin gwamnati mai suna Bala Musa ya shigar da kara a kotun yana zargin jarumar da kin auren sa duk kuwa da ya kashe mata kudi Naira dubu 360.
- Kotu ta ci dan sanda tarar N6m kan shiga gida babu izini
- Mahara sun kashe jami’an tsaro sun sace mutane a Kaduna
Aminiya ta ziyarci kotun a ranar Talatar da ta gabata, inda bagarorin biyu, mai kara da lauyansa da kuma wacce ake kara da lauyoyinta duk sun halarci zaman kotun.
Sai dai alkalin da ke sauraron karar, Khadi Rilwanu Kyaudai, ya nemi a dage zaman kotun saboda an sanar da shi rashin lafiyar matarsa.
A cewarsa, “Yanzun nan na samu labarin daya daga cikin matana an kai ta asibiti, don haka dole in kama hanyar Zariya a yanzu. Sai dai a saka wani rana domin a zo a ci gaba da zama,” inji shi.
Lauyan mai kara, Naira Murtala ya bayyana amincewarsa da dage zaman inda ya ce ko da sun ci gaba da zaman kotu ba lallai ba ne hankalin alkalin ya kasance yana tare da su.
Shi ma lauyan wacce ake kara, Barista Mubarak Sani Jibril, ya yi fatan samun lafiya ga matar alkalin tare da amincewa da sabon rana da aka saka domin ci gaba da sauraron karar.