An dage shari’ar Saraki
An dage shari’ar da ake wa Shugaban Majalisar Dattawa Abubakar Bukola Saraki da Mataimakinsa Ike Ekweremadu da tsohon Akawun Majalisa Salisu Maikasuwa da kuma Mataimakinsa Benedict Efeturi, zuwa ranar 28 ga watan Satumba mai zuwa. Ana tuhumar mutanen ne da kirkiro jabun dokokin majalisa. Kuma an shirya cewa yau Litinin ne za a ci gaba […]

An dage shari’ar da ake wa Shugaban Majalisar Dattawa Abubakar Bukola Saraki da Mataimakinsa Ike Ekweremadu da tsohon Akawun Majalisa Salisu Maikasuwa da kuma Mataimakinsa Benedict Efeturi, zuwa ranar 28 ga watan Satumba mai zuwa.
Ana tuhumar mutanen ne da kirkiro jabun dokokin majalisa. Kuma an shirya cewa yau Litinin ne za a ci gaba yi musu shari’a a wata babbar kotu da ke Abuja.
Duk da cewa kotun ba ta yi zama ba, amma duka mutanen da ake tuhuma sun halarci kotun gabanin su fahimci cewa an dage zaman.
Har ila yau, an bayyana cewa an dage zaman ne “saboda kotuna sun fara hutu.”