An dage shari’ar yi wa ’yar shekara 12 ciki a Jigawa

Kotun lardi ta shari’ar Musulunci da ke Karamar Hukumar Garki a Jihar Jigawa a karkashin jagorancin mai shari’a Aliyu Haruna Roni ta dage sauraron karar da wata yarinya mai suna Firdausi Abdulmumini ta shigar gabanta tana neman kotun ta tursasa Malam Yahai Maigatarin Bawan Allah ya amshi dan da suka haifa ba tare da aure […]

An dage shari’ar yi wa ’yar shekara 12 ciki a Jigawa
An dage shari’ar yi wa ’yar shekara 12 ciki a Jigawa

Kotun lardi ta shari’ar Musulunci da ke Karamar Hukumar Garki a Jihar Jigawa a karkashin jagorancin mai shari’a Aliyu Haruna Roni ta dage sauraron karar da wata yarinya mai suna Firdausi Abdulmumini ta shigar gabanta tana neman kotun ta tursasa Malam Yahai Maigatarin Bawan Allah ya amshi dan da suka haifa ba tare da aure ba.
Kotun ta dage sauraren karar ce saboda rashin halartar shaidun dan sanda mai gabatar da kara a gabanta sai zuwa ranar Juma’a (4/3/2016), domin zartar da hukunci sakamakon bukatar hakan da dan sandan ya yi, bukatar da ta samu amincewar lauya mai kare wadanda ake tuhuma na daya da na biyu.
Sai dai lauyan mai kara da wani matashi da aka ce yana cikin wadanda suka yi mata cikin ya bukaci alkalin kotun da ya aike wa wadanda aka ce shaida ne su san ranar da za a sake zama a kotun domin a kammala shari’ar kowa ya huta. Ya ce rashin sanar da su da wuri na iya kawo tarnaki ko tsaiko ga shari’ar.  Lauya M.M. Taura ya ce akwai bukatar kotun ta taimaka wajen kawo karshen shari‘ar saboda ya lura duk bangarorin biyu sun ji jiki kan shari’ar.