An dage shari’ar zargin Rarara da taurin bashin N10m
Lauyan Rarara ya ce zargin da ake wa mawakin tamkar wani labari ne da aka kirkira
Babbar Kotun Muslinci da ke Rijiyar Zaki a Kano ta fara da sauraron shari’ar zargin mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara da taurin bashin sama da Naira miliyan 10 da wani dan kasuwa ke masa.
Duk da cewa mawakin bai halarci zaman ba, mai kara, Muhammad Ma’aji ya bayyana wa kotun irin manyan wayoyin iPhone da mawakin ya yi ta karba bashi a wajensa yana raba wa wadanda suka ci wata gasar waka da ya sanya.
- An kashe mana mutum 89 cikin wata 3 —Al’ummar Apa
- Shugaban masu rinjaye na Majalisar Kogi ya yi murabus
A cewar dan kasuwar, akwai kuma kundin datan Rarara da matansa da kudin katin kallo da yake saka wa iyalan Rarara na tsawon lokaci ba a biyan sa, amma duk lokacin da ya yi magana sai mawakin ya ba shi hakuri.
Ma’aji ya kara da cewa ya shekara guda yana bin duk hanyoyin da suka kamata ya bi, amma mawakin ya ki biyan sa kudin, kuma duk wadanda ya yi wa magana su sa baki, cewa suka harkar siyasar mawakin ce a gabansa.
Bayan karanta wannan zargi na taurin bashi, lauyan Rarara, Barista I. Badawi, ya ce ba su gamsu ba, domin kuwam tamkar wani labari ne aka zo aka kirkira a gaban kotun, saboda haka ya bukaci alkali ya ba su lokaci don yin nazari a kai.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Halhalatulkuza’i Zakariya, ya dage cigaba da sauraran shari’ar zuwa ranar Litinin 17 ga watan Afrilu da muke ciki.
A baya dai sau biyu ana aike wa da jami’an kotun domin su mika wa mawakin takardar sammaci daga kotu, amma har aka zo zaman sauraran shari’ar na farko mawakin bai zo ba bai kuma turo ba, sai a zama na biyun nan da lauyansa ya bayyana.