An dage taron Manyan Hafsoshin Tsaron ECOWAS kan matakin soji a Nijar

Al’ummar Nijar sun yi zanga-zangar adawa da shirin ECOWAS na amfani da ƙarfin soji a kasarsu

An dage taron Manyan Hafsoshin Tsaron ECOWAS kan matakin soji a Nijar

Sojojin Senegal a taron shugabannin ECOWAS kan juyin mulkin Nijar Abuja, rana 10 da Agusta, 2023. (Hoto by KOLA SULAIMON /AFP)

An ɗage taron manyan hafsoshin tsaron ECOWAS da aka shirya gudanarwa ranar Asabar kan umarnin da ƙungiyar ta ba su na ɗaukar matakin soji a Nijar.

An dage zaman taron sai abin da hali ya yi duk kuwa da cewa ƙungiyar ta umarci manyan hafsoshin nata da su kafa rundunar ko-ta-kwana kwana domin murƙushe juyin mulkin Nijar da kuma dawo da Shugaba Mohamed Bazoum kan kujerarsa.

Kafin dagewar an shirya taron ne a birnin Accra ba ƙasar Ghana, domin manyan hafsoshin hafsoshin su yi wa ƙungiyar ECOWAS bayanin hanya mafi dacewa wajen amfani da rundunar ko-ta-kwanan da za a tura Nijar.

Sai dai a ranar Juma’a dubban al’ummar Nijar sun gudanar da zanga-zangar adawa da shirin ECOWAS na amfani da ƙarfin soji.

Masu zanga-zangar ɗauke da tutar ƙasar Rasha sun yi tattaki zuwa wani sansanin sojin Faransa da ke birnin Yamai inda suke wake-wake da daga kwalaye masu ɗauke da rubutun sukar Faransa da ECOWAS.

A gefe guda kuma, ƙasashen Turai da kungiyar Tarayyar Afirka na nuna damuwa game da halin da hamɓararren Shugaban Kasa Mohamed Bazoum yake ciki a hannun masu juyin mulkin da ke tsare da shi tun ranar 26 ga watan Yuli da suka kifar da gwamnatinsa.

Sojojin sun yi barazanar hallaka Bazoum idan aka kai musu hari, a yayin da gwamnatocin sojin ƙasashen Mali da Burkina Faso da ke makwabtaka da su suka yi alkawarin taimaka musu.

Daga baya aka sanar da ɗage zaman sai abin da hali ya yi, saboda wasu dalilai.

Zuwa yanzu dai ECOWAS ba ta fitar da jadawali ko fayyace yanayin ƙarfin sojin da dakarun nata za su yi amfani da shi a Nijar wajen murƙushe juyin mulkin ba.

Hakazalika har yanzu shugabannin ƙungiyar sun bayyana cewa sun fi son amfani da hanyar alama wajen ganin an dawo da gwamnatin farar hula a Nijar.

Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar na zargin tsohuwar uwar gijiyar ƙasar Faransa, wadda ke ɗasawa da gwamnatin Bazoum da hura wa ECOWAS wuta wajen ɗaukar matakin soji a ƙasar.

Masu zanga-zangar da na bayyana goyon baya ga jagoran juyin mulkin, Janar Abdourahamane Tchiani, inda suke zargin ECOWAS da zama ’yar amshin shatar Faransa.

Faransa na da sojoji 1,500 a Nijar ƙarƙashin yarjejeniyar haɗin gwiwarta da Gwamnatin Bazoum wajen yaƙar ’yan ta’adda masu iƙirarin jihadi da kusan shekara takwas suna addabar ƙasar.

Yanzu Faransa na fuskantar karin baƙin jini a yankin Sahel, inda ko a bara sai da ta kwashe sojojinta daga ƙasar Burkina Faso da kuma Mali bayan sojojin da suka yi wa ’yan siyasa juyin mulki a ƙasashen biyu sun raba gari da ita.

A makon jiya sojojin Nijar suka soke yarjejeniyar tsaro da gwamnatin Bazoum ta kulla da Faransa, bayan harin da masu zanga-zanga suka kai wa ofishin jakadancin Faransa a Yamai a ranar 30 ga watan Yuli ya sa ta kwashe ’yan ƙasarta daga Nijar.