An dage zaben kananan hukumomin Jihar Katsina

Hukumar Zabe ta Jihar Katsina ta dage zaben kananan hukumomin jihar da ta shirya gudanarwa ranar 2 ga Agusta zuwa ranar 6 ga Satumba mai zuwa.Shugaban hukumar Alhaji Abubakar Lawal Malumfashi ya shaida wa manema labarai haka a ranar Talata inda ya ce, hukumar ta yi haka ne saboda korafe-korafe da kiraye-kirayen da ta samu […]

An dage zaben kananan hukumomin Jihar Katsina
An dage zaben kananan hukumomin Jihar Katsina

Hukumar Zabe ta Jihar Katsina ta dage zaben kananan hukumomin jihar da ta shirya gudanarwa ranar 2 ga Agusta zuwa ranar 6 ga Satumba mai zuwa.
Shugaban hukumar Alhaji Abubakar Lawal Malumfashi ya shaida wa manema labarai haka a ranar Talata inda ya ce, hukumar ta yi haka ne saboda korafe-korafe da kiraye-kirayen da ta samu daga wasu jam’iyun siyasa da masu ruwa da tsaki kan bayar da kwana 60 don gudanar da zaben maimakon kwana 90 da doka ta tanada.
Alhaji Abubakar Malumfashi ya ce, hukumar ta kuma rage kudin cike takardun tsayawa takara da kashi zuwa rabi, inda ya bukaci jam’iyyun siyasa su bi dokoki da ka’idojin zaben don samun sahihin zabe.
Ana ganin daukar wannan mataki bai rasa nasaba da kaurace wa zaben da babbar jam’iyyar adawa ta APC ta yi da barzanar zuwa kotu, sai kuma yadda a baya-bayan nan Jam’iyyar LP ta musanta shigarta zaben, yayin da ake rade-radin ita PDM ta ce ba za ta shiga zaben ba.
 Jam’iyyar APC a Jihar Katsina ta shaida wa manema labarai a ranar Talatar cewa tuni ta garzaya Babbar Kotun Tarayya da ke Katsina don shigar da kara kan a hana gudanar da zaben.
Shugaban jam’iyyar Dokta Mustafa Inuwa yace, sai da suka rubuta wa hukumar zaben ta gyara amma ta ki, hakan ya sa suka garzaya kotu domin a bi dokar zabe.
Shugaban ya ce, abin da suke bukata shi ne, a dakatar duk wani abu da ya shafi zaben a sanya hukumar zabe ta nemo dukkan jam’iyyu a zauna da su a sake jadawalin zabe bisa ga dokokin zabe na jihar da na tarayya da tsarin mulki ya bayar.
Dokta Inuwa ya ce, APC ta fi kowa son a yi zaben, saboda tana da yakinin samun nasarar da za ta kawo canji a kananan hukumomin da ya ce an bar su a baya babu ci gaba bayan wata karamar hukumar na samun har naira miliyan 150.