An dai ji kunya
Idan har bajimin sa na tsaye da wuya a tunkare shi, amma idan ya fadi sai kowa ya janyo wukarsa ta yankan nama. Wadannan kalamun sun yi daidai da Najeriya, kasar da a ’yan shekarun baya ta zame giwar Afirka, sauran kasashen kuma ke kiran ta yaya babba. Dalili kuwa shi ne ta nuna masu […]
Idan har bajimin sa na tsaye da wuya a tunkare shi, amma idan ya fadi sai kowa ya janyo wukarsa ta yankan nama. Wadannan kalamun sun yi daidai da Najeriya, kasar da a ’yan shekarun baya ta zame giwar Afirka, sauran kasashen kuma ke kiran ta yaya babba. Dalili kuwa shi ne ta nuna masu halaye irin na karimci da dattaku har ta kai ita ce ke shiga tsakaninsu idan suna tankiya, ita ce kan gaba wajen agaza masu idan sun shiga mawuyacin hali. Amma a yanzu Najeriyar ce ake taruwa ana agazawa; kasashen da suka amfana da ita sun komo daga rakiyarta; ta susuce, ba ta iya sanya wa, ba ta kuma iya hana wa, walau a cikin gidanta ko a kasashen makwabta.
A takaice dai ana iya cewa Najeriyar yanzu godiya ce wacce ta durkushe da sirdinta, kuma batan basira ya samu shugabanninta har sai da ta kai sun bar rashawa ta yi kaka-gida, tana dagula dukkan al’amuranta. Sun kuma bar ’yancin da shugabanninta na farko suka yako daga miyagun Turawa ya balbalce, mutuncin kasar kuma ya zube warwas a idanun duniya
Wannan mummunan al’amarin ya zame tamkar cin kwan makauniya, ya ki ci, ya kuma ki cinyewa, kuma sai ga shi nan rashin tsaro ya kunno kai, aka kuma kawar da kai game da haka, har sai da ya habaka, ya gagari shugabanni, aka samu rashin lumana talakawa kuma suka kasa zaman lafiya. Tun daga lokacin da sojoji suka yi ban-kwana da mulki a shekarar 1999, Najeriya ba ta zauna lafiya ba, kuma ya zuwa yau jama’ar kasar, musamman ma a nan yankin Arewa sun yaba wa aya zaki, sun kuma zaku a samu canjin yanayi, amma duk a banza.
Talakawan Najeriya suna ji, suna gani shugabannin gwamnatocinsu da na majalisun dokoki suna debo ruwan dafa kansu da kansu, su kuma jama’ar kasar na kara iza wutar da aka hura ta da guma-guman kabilanci da na addini, kasashen duniyar da suka haddasa haka kuma don kai wa ga biyan munanan bukatunsu suna ta tsallen murnar tarkonsu ya kama masu naman miya. Ana cikin haka ne Turawa suka kara ruruta waccan wutar ta hanyar kirkiro kungiyoyin ta’addanci da sunan addini don su samu kafar kutsowa kasar su idar da munanan manufofinsu. Shi ya sa fitintunun da suka haddasa mana, tare da shugabannin da ba su kishin kasarsu, ba su kuma tausayin jama’arsu suka bi suka addabe mu har sai da muka nemi taimakonsu don magance illolinsu, alhali kuwa kura ce aka ba ajiyar nama.
An nemi su taimaka, sun kuma motsa don taimakawar, amma tun tafiya ba ta kai ko ina ba an fahimci cewa burinsu ba shi ne taimaka wa Najeriya fita daga kangin da suka jefa ta ciki ba. Su burinsu shi ne arzikin da Buwayi Ya huwace mana da kuma tunanin hanyar da za su bi su fi jama’ar kasar cin gajiyarsa. Shi ya sa ko da suka zo, bayan amsa gayyata da zimmar zakulo ’yan matan makarantar Chibok sama da dari biyu da hamsin da kuma dakile kungiyar Boko Haram, babu abin da ya faru domin ba wannan ne a gabansu ba, tunaninsu da aikace-aikacensu sun wuce nan. Su yanzu arzikin man da ke jibge a yankin Neja Delta suke hange, kuma can za su dosa don su kashe kishinsu.
To amma babban abin takaici game da haka ba gayyatar da aka yi wa wadannan Turawa ce ba, sai dai yadda Turawan, musamman kasar Ingila da ta reni Najeriya da Faransa da ta reni makwabtanta guda hudu, suka kasa takura masu don su hada kai su magance dukkan matsalolin tsaron da ake cewa sun addabi Najeriya. Maimakon a ce kasashen Kamaru da Chadi sun hada kai da Najeriya wajen magance masifar Boko Haram sai cewa ma ake yi suna da hannu wajen gawurtar kungiyar, domin kuwa da sanin uwargidansu Faransa tunzurin ‘yan ta’addan Najeriya da ke makwabtaka da yankin Tafkin Chadi da Kamaru ya yi kamari. Daga cikinsu babu wacce Najeriya ba ta yi ruwa, ta yi tsaki ba wajen murkushe tawaye ko ta’addancin da suka faru a kasashensu, alhali kuwa kasar Faransa ce ummul-haba’isin afkuwarsu. To tun da haka ne kuwa me ya hana gwamnatin Najeriya kiran shugabannin kasashen Nijar da Kamaru da Chadi zuwa Najeriya tun can farko don tattauna matsalolin kungiyar Boko Haram,ta kuma matsa masu don taimakawa a murkushe su,’ ko da kuwa su ba su yi mata tayin haka ba domin su ramawa kura aniyarta na baya? Najeriya ba ta yi haka ba domin kasashen Ingila da Amerika ba so suke yamutsin ta’addancin da suka taimaka don afkuwarsa ya yi saurin karewa ba, kamar yadda suka hana kungiyar hada kan kasashen Afrika tsoma bakinta cikin kokarin da ake yi don murkushe ta’addancin kungiyar Boko Haram.
kasashen Afrika dai sun ji kunya tun da ba su iya sasanta tsakaninsu, ko su hada kai su yi maganin kutungwilar Turawan da suka hana nahiyarsu kokartawa don kai wa ga kasaita. Ga shi nan yanzu Faransa ta nuna wa duniya cewa Najeriyar da suke takama da ita ba komai ce ba domin ta zama mushen gizaka.