An daina biyan tallafin man fetur, za a ci gaba da amfani da tsoffin takardun Naira —Tinubu

Biyan tallafin man fetur ba ya fidda a’i daga rogo. 

An daina biyan tallafin man fetur, za a ci gaba da amfani da tsoffin takardun Naira —Tinubu

Tinubu

Shugaban Kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa a yanzu biyan tallafin man fetur a kasar ya zama tarihi kasancewar ba ya fidda a’i daga rogo. 

Tinubu wanda ya bayyana hakan bayan shan rantuswar kama aiki a matsayin Shugaban Najeriya, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta ci gaba da biyan tallafin man ba sabanin yadda gwamnatin da ta gabata ta yi.

A jawabinsa bayan shan rantsuwa a Dandalin Eagle Square da ke Abuja, Tinubu ya bayyana cewa za a ci gaba da amfani da tsofaffin takardun naira kafada-da-kafada da sabbin takardun kudin.

Kazalika, ya ce gwamnatinsa za ta yi nazari kan sauya fasalin takardun kudin wanda gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta aiwatar.

A cewarsa, “Mun yaba wa matakin da gwamnati mai barin gado ta dauka na kawar da tsarin biyan  tallafin man fetur wanda mun lura ya masu hannu da shuni sun fi cin moriyarsa fiye da talakawa.

“Tallafin man fetur da ake biya ya gaza tabbatar da fa’idarsa, a maimakon haka, za mu karkatar da akalar kudaden da muke biya wajen aiwatar da wasu ayyukan musamman zuba jari a cikin inganta ababen more rayuwa na jama’a, ilimi, kiwon lafiya da ayyukan yi wadanda za su inganta rayuwar miliyoyin jama’a.

“Sannan duk wata fa’ida da tsarin sauya fasalin takardun kudi ya kunsa, Babban Bankin Najeriya CBN bai yi la’akari da kuncin da al’umma za su fusukanta ba wajen karbar tsarin a yayin da akwai dimbin jama’ar da ba sa kowace irin harkalla da banki ko bude asusun.

“Saboda haka za mu yi nazari a kan wannan batu, amma kafin nan gwamnatinmu za ta ci gaba da amfani da tsofaffi da sabbin takardun kudin a lokaci guda.”