An dakatar da alkalai 3 a Kano kan almundahana

Hukumar Shari’a ta Jihar Kano (JSC) ta dakatar da alkalan Kotun Majistare uku kan laifin sakaci da kuma almundhana yayin gudanar da ayyukansu.

An dakatar da alkalai 3 a Kano kan almundahana

Hukumar Shari’a ta Jihar Kano (JSC) ta dakatar da alkalan Kotun Majistare uku saboda samun su da laifi a yayin gudanar da ayyukansu.

Kakakin kotunan jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim, ya sanar cewa an dakatar da alkalai uku daga ayyukan shari’a, yayin da aka bayar da ggargadi ga magatakardan kotu guda daya.

Alkalan da aka dakatar sun hada da Talatu Makama ta kotun Majistare Mai lamba 29, da Babbar Majistire Rabi Abdulkadir na Kotun Majistire mai lamba 48 da Alkalin kotun Majistire mai lamba 60, Tijjani Saleh Minjibir.

Na hudunsu shi ne  Magatakarda Abdu Nasir da ke sashin daukaka kara da ke Babbar Kotun Jihar Kano.

Sanarwar ta bayyana cewa kwamitin karbar korafe-korafen jama’a na bangaren shari’ar ya sami Alkali Talatu Makama da laifin rashin da’a inda ta bayar da umarni ga Bankin GT ya tura kudi zuwa asusun mai shigar da kara bayan ta san cewa asusun a rufe yake, inda daga karshe aka sanya kudi cikin asusunta.

Haka kuma Hukumar ta same ta da laifin nuna rashin kwarewa inda taje karbar shari’a tare da bayar da oda ga ’yan sanda tun kafin shari’ar ta zo gabanta.

“Saboda haka an sauke Babbar Alkali Talatu Makama daga  kujerarta an kuma dakatar da ita daga dukkan ayyukan shari’a nan take.

“Sai dai wannan bai shafi kasancewarta ma’aikaciyar gwamnati ba,” in ji sanarwar.

Takarda ta ci gaba da cewa, bayan binciken Hukumar ta JSC kan dambarwar shari’ar da ke tsakanin kwamishinan ’yan sanda da wani Abubakar Salisu da ke gaban Alkalin Kotun Majistare Mai lamba 48 Rabi Abdulkadir, an same ta da laifin yin sakaci a shari’a.

“Don haka hukumar ta dakatar da ita daga aikin shari’a na tsawon shekara guda.

“Sannan an umurce ta da ta daina duk wani aiki a Kotun Majistare mai lamba 48.”

Hukumar ta kuma dakatar da Alkalin Kotun Majistire mai lamba 60 Tijjani Saleh Minjibir na tsawon shekara daya bisa samun sa da laifin rashin da’a da rikon sakainar kashi ga harkar shari’a

“An dakatar da duk ayyukansa na shari’a na shekara daya sannan an umarce shi da komawa hedikwata domin sanar da shi wurin da zai yi aiki”.

Hukumar ta JSC ta kuma yi la’akari da rahoton binciken da ake zargin babban magatakarda Abdu Nasir na sashin daukaka kara na Babbar Kotun Jihar Kano.

“Rahoton ya tabbatar da cewa, Malam Nasir ya karbi kudaden da aka tanada na bayanan kotu a cikin asusunsa na kashin kansa, wanda hakann ba daidai ba ne.

“Sakamakon haka Hukumar ta yi wa Abdu Nasir gargadi mai karfi sannan ta dakatar da yi masa karin girma da shekara daya.”

Hukumar ta yi alkawarin ci gaba da daukar mataki kan duk ma’aikacin da ya yi kuskure musamman wadanda ke da nauyin shari’a a kansu domin kare mutunci da rikon amana na tsarin shari’a da kuma tabbatar da amincewar jama’a.

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya