An dakatar da Babban Akantan Jihar Kebbi
Gwamnatin Jihar Kebbi ta dakatar da manyan ma’aikatan kudi na jihar da suka hada da Mukaddashin Babban Akanta, Ibrahim Alkali wanda ke rikon kwarya a matsayin Babban Akantan Jihar, bayan Babban Akantan Jihar, Alhaji Ibrahim Zaki ya yi ritaya daga aiki. Haka kuma dakatarwar ta shafi Sakatariyar Asusun Hadaka na Jihar Kananan Hukumominta, Hajiya Saudatu […]
Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu
Gwamnatin Jihar Kebbi ta dakatar da manyan ma’aikatan kudi na jihar da suka hada da Mukaddashin Babban Akanta, Ibrahim Alkali wanda ke rikon kwarya a matsayin Babban Akantan Jihar, bayan Babban Akantan Jihar, Alhaji Ibrahim Zaki ya yi ritaya daga aiki.
Haka kuma dakatarwar ta shafi Sakatariyar Asusun Hadaka na Jihar Kananan Hukumominta, Hajiya Saudatu Abdullahi Yawuri.
Wata majiya ta bayyana wa Aminiya cewa Gwamnan Jihar ne ya bayar da umarnin dakatar da Mukaddashin Babban Akantan da kuma Sakatariyar Assusun Hadakar saboda matsalar da ke da alaka da assusun hadakar na kananan hukumomin jihar.
Bayan dakatar da wadannan manyan jami’ai, kuma an kafa kwamitin mutum biyar domin bincikensu. Tsohon Babban Mai Binciken Kudi na Jihar Kebbi, Alhaji Yaro Kakale Kalgo ne aka nada shugaban kwamitin.
Domin jin ta bakin Gwamnatin Jihar Kebbi, wakilinmu ya tuntubi Kwamishinan Watsa Labarai da Al’adu na Jihar, Alhaji Muhammad Gado Marafa inda ya ce, ba ya da masaniya kan dakatar da manyan ma’aikatan biyu, domin ba ya cikin jihar ta Kebbi kimanin mako biyu da suka gabata.