An dakatar da basarake kan yin liki da takardun Naira a Ogun

Masarautar Egba ta dakatar da Olu na Owode, Oba Kolawole Sowemimo, saboda ya yi wa mawaki liki da takardun Naira.

An dakatar da basarake kan yin liki da takardun Naira a Ogun

Masarautar Egba da ke Jihar Ogun ta dakatar da Olu na Owode da ke Karamar Hukumar Obafemi/Owode, Oba Kolawole Sowemimo, saboda wulakanta takardun Naira.

Majalisar Masarautar Egba, karkashin jagorancin Alake na Kasar Egba, ta dakatar da Olu na Owode daga sarauta ne bayan da wani bidiyonsa ya karade gari, wanda a ciki yake yi wa wani mawaki liki da takardun Naira a wurin wani biki.

A cikin bidiyon kuma, an ga basaraken da wata igiya da aka hada da takardun Naira 1,000, ya nada wa fitaccen mawakin kasar yarbawa, Wasiu Ayinde, wanda aka fi sani da KWAM 1.

A watan da ya gabata ne Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA) ta rubuta wa basaraken wasika cewa ce abin da ya yi zai iya sa a daure shi.

A ranar Juma’a kuma Majalisar Masarautar Egba ta sanar da dakatar da shi kan cin mutuncin kudin Najeriya a bainar jama’a, wanda laifi ne a doka.

Majalisar ta dakatar da shi na tsawon watanni biyu ba tare da albashi ba, bayan shawarar kwamitinta na da’a wanda ya bayyana cewa a tsawon wa’adin dakatarwar, an haramta masa gabatar da kansa a matsayin basarake.

Hakazalika an haramata gayyatar sa zuwa kowane irin sha’anin gwamnati ko na al’umma a matsayin sarkin gargajiya, kuma ba za a biya shi ko sisi ba.
Da yake tabbatar da dakatarwar da aka yi masa, Oba Sowemimo ya ce “An sanar da dakatarwar ne a ganawar da muka yi a jiya (Juma’a), saboda yadda na yi wa mawakin liki.

“Da aka tambaye ni ko akwai wani abu da zan ce, sai na mike na ba da hakuri kan duk abin da na aikata ba daidai ba, kuma dakatarwar da aka ce za ta yi na tsawon watanni uku ba tare da albashi ba ta koma wata biyu.

“Na amince da hukuncin da aka yanke.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos