An dakatar da dagaci da kansila kan satar taransifoma a Gombe

An dakatar da mutanen biyu daga muƙamansu ne domin bayar da damar gudanar da bincike yadda ya dace.

An dakatar da dagaci da kansila kan satar taransifoma a Gombe

Gwamnatin Jihar Gombe ta dakatar da dagacin garin Majidadi da ke yankin Ƙaramar Hukumar Akko, Mohammed Majidadi bisa zargin hannu a sace wata taransifoma.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ya fitar a wannan Juma’ar.

Sanarwar wadda Sakataren Yaɗa Labarai na Fadar Gwamnatin Gombe, Isma’ila Uba Misilli ya sanyawa hannu, ta ce an kuma dakatar da kansilan mazaɓar Kumo ta Gabas, Abdullahi M. Panda bisa wannan zargi.

A baya-bayan nan ne dai rundunar ’yan sandan jihar ta yi holen mutanen biyu da ta ce ta kama bisa zargin haɗa baki da ɓarayi wajen sayar da taransifomar lantarkin Garin Majidadi.

Sanarwar ta ce an dakatar da mutanen biyu daga muƙamansu ne domin bayar da damar gudanar da bincike yadda ya dace.

Gwamnan Jihar Inuwa Yahaya ya ce yana da ƙwarin gwiwa doka za ta yi aiki a kan mutanen idan aka same su da laifin da ake tuhumarsu da shi.

Gwamna ya ƙara da cewa baya ga mutanen biyu, duk wanda aka samu da hannu a sayar da taransifomar zai fuskanci hukunci.