An dakatar da dagaci kan zargin saran maraya da adda
Aminiya ta ruwaito yadda raunukan marayan mai shekara 15 suka fara ɗoyi saboda rashin samun kulawa bayan asibiti sun ƙi karbarsa saboda rashin kuɗi,
![An dakatar da dagaci kan zargin saran maraya da adda An dakatar da dagaci kan zargin saran maraya da adda](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2024/07/Adda.jpg)
An dakatar da Dagacin Karagawal da ke Jihar Gombe, Usman A. Bello, daga kujerarsa, har sai an kammala bincike kan zargin da ake masa na saran wani maraya da adda har sau bakwai.
A baya Aminiya ta ruwaito yadda jikin marayan, mai suna Adamu Muhammad mai shekara 15 ya fara ɗoyi saboda rashin samun kulawa bayan asibiti sun ƙi karbarsa saboda rashin kuɗi, sakamakon raunukan da yake zargin dagacin ya yi masa.
A yayin hirar da Aminiya ta yi da shi a lokacin, Dagacin ya musanta sarar yaron, inda ya bayyana cewa ya yi ƙoƙarin kare kansa ne bayan varayi ɗauke da makami sun shiga gidansa.
Lamarin da ya faru a farkon watan Disamba na shekarar 2024, wanda ya haifar da ce-cekuce a yankin.
- ‘A sansanin gudun hijira na yi sakandare har na zama likita’
- Jirgin Amurka ɗauke da mutum 10 ya ɓace
Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, Barista Sani A. A. Haruna, ya bayyana cewa an dakatar da basaraken ne domin tabbatar da adalci da kuma kare martabar duk wanda lamarin ya shafa.
Ya ce, “Mun ɗauki xawainiyar jinyar yaron, inda muka kashe sama da Naira dubu ɗari biyar. Wannan nauyi ne na gwamnati, ba iyayensa ba, domin ba shi ya ji wa kansa ciwo ba.”
Barista Haruna ya ce an dakatar da Dagacin ne bayan ƙorafin da aka samu cewa ya ɗauki matakin da ya saba wa doka, “ko da yaron ya aikata wani laifi, ba ya halatta a xauki doka a hannu. A maimakon haka, doka ta tanadi cewa a kai shi gidan horon yara. Amma abin da ya fi muhimmanci a yanzu shi ne tabbatar da cewa yaron ya samu sauqi kafin a ci gaba da bincike.”
Dagacin Karagawal, Usman A. Bello, ya kare kansa da cewar wasu matasa ne suka shiga gidansa da makamai cikin dare da nufin sata, wanda hakan ya sa shi ɗaukar matakin kare kansa.
Ya ce, “Na samu nasarar qwace adda daga ɗaya daga cikinsu, sannan na yi amfani da ita don kare kaina.’
A daya bangaren, saurayin aka yi wa raunin, Adamu Muhammad, ya musanta daukar makami ko aikata sata. Ya ce, “Na shiga gidan ne ba tare da izini ba, amma Dagacin ne ya zo da adda ya sassara ni har na ji ciwo a wurare daban-daban.”
Idan ba a manta ba, a baya yaron ya shaida wa wakilin Aminiya cewa ya je neman mafaka a gidan dagacin ne saboda tsoron matakin da mahaifiyarsa za ta xauka a kansa bayan ya yi faɗa da wata budurwa a makwabtansu, har ta kai ƙararsa wurin ’yan banga, suka nemi ya biya yarinyar kuɗi, kuma ba shi da su.
Shugaban ƙaramar hukumar ya ce za a gudanar da cikakken bincike ba tare da nuna son kai ba. Ya ce, “Ba za mu yanke hukunci yanzu ba, har sai mun saurari bayanin yaron da zarar ya samu lafiya.
“Idan aka yanke hukunci yanzu kuma daga baya wani abu ya taso, misali rashin lafiyarsa ko wani akasin haka, to shari’ar za ta canza gaba ɗaya.”
Ya kara da cewa matakin dakatar da Dagacin ya ba da damar gudanar da bincike cikin gaskiya da adalci. “Idan bincike ya tabbatar da cewa Dagacin ne ya yi wa yaron rashin adalci, to za a xauki matakin da ya dace. Idan kuma aka gano cewa yaron ne da laifi, za a yi hakan cikin tsari.”