An dakatar da hakimai 4 saboda saba wa dokar Hawan Sallah a Zazzau

Ana zargin hakiman da saba doka ta uku da ke cikin kundin laifukka da hukunce-hukuncen hawa a Masarautar Zazzau.

An dakatar da hakimai 4 saboda saba wa dokar Hawan Sallah a Zazzau

Sarkin Zazzau na 19, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli a wurin bikin nadinsa.

Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya dakatar da hakimai hudu na Masarautar Zazzau daga mukamansu.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Fadar Zazzau, Abdullahi Aliyu Kwarbai ya fitar jim kadan bayan sauka daga hawan sallah da aka gudanar a ranar Litinin.

BBC ya ruwaito cewa an dakatar da hakiman ne bisa saba dokokin da aka gindaya na Hawan Sallah.

Hakiman da aka dakatar sun hada da Ubangarin Zazzau Alhaji Bashir Shehu Idris da Wakilin Birnin Zazzau Alhaji Suleiman Ibrahim Dabo da Sarkin Dajin Zazzau Alhaji Shehu Umar da kuma Garkuwan Kudun Zazzau Alhaji Muhammadu Sani Uwais.

Ana zargin hakiman da saba doka ta uku da ke cikin kundin laifukka da hukunce-hukuncen hawa a Masarautar Zazzau wadda ta haramta wa kowane hakimi yin hawa da ’yan tauri rike da makamai.