An dakatar da hakimi saboda yi wa wata auren dole a Neja

Ana tuhumar shi da laifin yi wa wata yarinya auren dole tare da cin zarafin mahaifinta.

An dakatar da hakimi saboda yi wa wata auren dole a Neja

Masarautar Minna da ke Jihar Neja ta tunbuke rawani tare da dakatar da Hakimin Allawa, Mallam Bello Haruna, kan kama shi da laifin tilasta yin auren dole.

Masarautar cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakatarenta, Usman Umaru Guni, ta ce an kama hakimin da laifin yi wa wata yarinya auren dole da cin zarafin mahaifinta, tare da sa ’yan banga su lakada mata dukan kawo wuka.

Kazalika, an tuhumi hakimin da kin amsa goron gayyata da masarautar ta aike masa don amsa tambayoyi game da zarge-zargen da ake masa.

Sarkin Minna, ya ce hakimin bai nuna halin dattako da halaye masu nagarta ba wajen jagorantar al’ummar yankin da ya ke mulka a Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Masarautar ta sanar da nadin Galadiman Allawa, Ahmadu Magaji a matsayin hakimin wucin gadi na yankin kafin kammala bincike.