An dakatar da ita daga aiki don ta ki raba barasa
A karshen makon jiya ne wata Ba’amurkiya Musulma ta shigar da koke a gaban hukumar kare hakkin ma’aikatan kasar Amurka, bayan da ta ce an dakatar da ita daga aikinta domin ta ki raba barasa, kamar yadda gidan talabijin na CNN ya ruwaito.Matar mai suna, Charee Stanley, mai shekara 40, tana aikin raba abinci a […]
A karshen makon jiya ne wata Ba’amurkiya Musulma ta shigar da koke a gaban hukumar kare hakkin ma’aikatan kasar Amurka, bayan da ta ce an dakatar da ita daga aikinta domin ta ki raba barasa, kamar yadda gidan talabijin na CNN ya ruwaito.
Matar mai suna, Charee Stanley, mai shekara 40, tana aikin raba abinci a cikin jirgin sama ne da kamfanin EdpressJet. Kuma ta ce ta yi hakan ne saboda ya ci karo da koyarwar addininta.
Kamar yadda lauyanta mai suna, Lena Masri ya ce ga alama kamfanin bai yi niyyar daukar wani mataki ba da farko. Lauyan ya ce, “saboda lokacin da ta ki raba barasar an ce mata za a sanya wata ta yi hakan, amma daga bisani sai kuma aka tura ta hutun dole na tsawon shekara guda ba tare da biyanta ko sisi ba daga albashinta. Ka ga ke nan an musguna mata saboda addininta, ” inji shi.
Kodayake, kamfanin ya fitar da wata sanarwa, wadda a cikinta yake cewa yana martaba tanade-tanade kowane addini, amma sai ya ki cewa komai daga nan.
Mis Charee dai ta shafe shekara uku tana aiki da kamfanin, kuma ta Musulunta ne a bara. Kodayake, ta ce sai a farkon bana ne ta fahimci cewa addininta ya hana ta tu’ammali da barasa. Kuma daga nan sai ta ce ta ja layi.