An dakatar da karin kudin shiga Intanet

An dakatar da shirin kara kudin shiga Intanet wato Data ga masu amfani da wayar salula, kamar yadda Hukumar da ke Kula da Kamfanonin Sadarwa (NCC ) ta bayyana. Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Tony Ojobo ya aikewa manema labarai, ya ce sun dauki matakin ne sakamakon sukar da suke sha daga […]

An dakatar da karin kudin shiga Intanet
An dakatar da karin kudin shiga Intanet

An dakatar da shirin kara kudin shiga Intanet wato Data ga masu amfani da wayar salula, kamar yadda Hukumar da ke Kula da Kamfanonin Sadarwa (NCC ) ta bayyana.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Tony Ojobo ya aikewa manema labarai, ya ce sun dauki matakin ne sakamakon sukar da suke sha daga wurin jama’a.

“Hukumar ta umarci kamfanonin sadarwa su dakatar da kara kudin  kan masu amfani da su,” inji shi.

A makon jiya ne hukumar ta bai wa kamfanonin sanarwar umarnin kara kudin da suke sayar da Data zuwa kwabo 90 kan kowanne Mega bite daga gobe Alhamis wato 1 ga watam Disamba.

Sai dai ‘yan Najeriya sun soki matakin, suna maus cewa wani yunkuri ne na hana su fadar albarkacin bakinsu.