An dakatar da kungiyar sintirin Jihar Gombe
Rundunar ’yan sandan Jihar Gombe ta dakatar da duk wani aikace-aikacen kungiyar ’yan sintiri a duk fadin jihar bayan zargin su da kashe wani dalibi. Jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Fwaji Atajiri, ne ya sanar da hakan a madadin Kwamishinan ‘yan sandan jihar Abdullahi Kudu Nma, a wata takarda mai dauke da sanya […]
Rundunar ’yan sandan Jihar Gombe ta dakatar da duk wani aikace-aikacen kungiyar ’yan sintiri a duk fadin jihar bayan zargin su da kashe wani dalibi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Fwaji Atajiri, ne ya sanar da hakan a madadin Kwamishinan ‘yan sandan jihar Abdullahi Kudu Nma, a wata takarda mai dauke da sanya hannunsa da ya aike wa manema labarai, wadda take bayyana cewa rundunar ta soke ayyukan kungiyar ne saboda yadda suke gudanar da ayyukansu “ba tsari kuma suke daukar doka a hannunsu.”
Takardar ta ce wani bincike da jami’an ’yan sanda suka yi ya nuna cewa: “kungiyar ’yan sintirin suna ayyukansu ne ba bisa ka’ida ba ta hanyar tsare mutane ta hanyar da ba ta dace ba.”
Sanarwar ta kara da cewa: “A watan jiya ne ’yan bangan suka tsare wani dalimin Kwalejin Horar da Malamai ta Gwamnatin Tarayya, mai suna, Usman Abubakar, ba bisa ka’ida ba. Ana zargin su gana masa azaba har ya mutu a hannunsu.
Daga nan sanarwar ta bayyana cewa ’yan sanda sun fara gudanar da bincike kan al’amarin kuma tuni suka kama wasu da ake zargi da hannu a kisan dalibin kuma da zarar sun kammala bincike za su turasu batun kotu.