An dakatar da Kwamishinan ’Yan Sandan Adamawa

An maye gurbinsa da Kwamishinan ‘Yan Sandan Gombe

An dakatar da Kwamishinan ’Yan Sandan Adamawa

Sufeto-Janar Usman Alkali Baba

Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya ba da umarnin dauke Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Adamawa, Mohammed Barde daga Jihar cikin gaggawa.

Kazalika, ya kuma umarci Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Gombe, Etim Equa, da ya karasa Adamawan ya rike ta har sai an bayyana sakamakon zaben Jihar.

Umarnin dai ya biyo bayan rawar da ake tunanin Barden ya taka lokacin da dakataccen Kwamishinan Zabe na Jihar ta Adamawa, Farfesa Hudu Yunusa Ari, ya bayyana sakamakon zaben Gwamnan Jihar tun ba a kammala tattara shi ba.

Farfesa Hudu dai, wanda a lokacin yake tare da Mohammed Barde dai ya bayyana Aisha Dahiru Binani ta APC a matsayin wacce ta lashe zaben.

Sai dai daga bisani INEC ta soke sanarwar tare da dakatar da Kwamishinan Zaben da kuma dakatar da ci gaba da tattara sakamakon.