An dakatar da lakcara saboda sa dalibai gwale-gwale a Kano

Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil a Jihar Kano ta dakatar a wani malaminta kan wahalar da dalibai.

An dakatar da lakcara saboda sa dalibai gwale-gwale a Kano

Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil a Jihar Kano ta dakatar a wani malaminta kan sa dalibai gwale-gwale.

Jami’in Hulda da Jama’a na jami’ar, Sa’idu Nayaya, ya sanar a ranar Laraba cewa an dakatar da malamin ne sakamakon wani bidiyonsa da ya karade kafofin yada labarai.

 A cikin bidiyon an ga malamin yana sa dalibai gwale-gwale a cikin aji saboda sun makara, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce da kiraye-kirayen neman taka masa burki. 

“Hakan ne ya sa aka dakatar da shi nan take aka mika lamarin ga kwamitin ladabtarwa na manyan malamai domin daukar matakin da ya dace.

“Hakan zai tabbatar da adalci da kuma hana sake faruwar irin haka a nan gaba.”

NAJERIYA A YAU: Dalilin Faɗuwar Farashin Tumatur A Kasuwa

An ƙaddamar wa ’yan kasuwa sabon tsarin biyan haraji a Gombe

Majalisa na son ƙirƙiro sabbin jihohi 31 a Najeriya

Malamai sun fara yajin aiki a Ebonyi