An dakatar da likita saboda watsi da mara lafiya a Kano
Hakan ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da majiyyata da ma’aikatan asibitin da aka samu bayan da likitar ta bar wurin marasa lafiyan
Babban Sakataren Hukumar Kula Da Asibitocin Jihar Kano (HMB), Dakta Mansur Mudi Nagoda, ya amince da dakatar da wata likita a Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase bisa zarginmta da yin watsi da marasa lafiya.
Wannan dai ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da majiyyata da ma’aikatan asibitin da aka samu bayan likitar ta bar wurin marasa lafiyan ba tare da sanar da mahukuntan asibitin ba.
- ’Yan bindiga sun kashe mace mai ciki da wasu 10 a Benuwai
- Hafsan Sojan Amurka Ya Yi Ritaya Don Goyon Bayan Falasdinawa
Ya bayyana cewa, an yi mata kiraye-kirayen da yawa amma ta ci gaba da cewa tana asibiti alhalin ba ta taɓa zuwa ba, wanda hakan ya sa majinyacin mai fama da cutar ƙoda a cikin wani mummunan hali.
Sakataren zartarwar ya jaddada cewa, “Za a ci gaba da sa ido sosai kuma muna sa ran duk wanda sunansa ya bayyana a ƙin yin aikin zai shafi aikinsa. Duk wanda aka samu yana irin wannan, to ya ɗora laifin a kansa”.
Dokta Nagoda ya yi nuni da cewa, likitocin sun yi rantsuwar kare rayuka, ya kuma buƙace su da su ruɓanya ƙoƙarinsu.