Rashawa: An dakatar da ma’aikatan Shari’a 6 a Kano

Hukumar Shari’a (JSC) ta ladabtar da wasu magatakardan kotuna su shida a Jihar Kano saboda samun su da laifuka daban-daban.

Rashawa: An dakatar da ma’aikatan Shari’a 6 a Kano

(Hoto: us.fotolia.com)

Hukumar Shari’a (JSC) ta ladabtar da wasu magatakardan kotuna su shida a Jihar Kano saboda samun su da laifukan cin rashawa.

Sanarwa da Kakakin Kotunan Jihar Kano Baba Jibo Ibrahim ya sanya wa hannu, ta ce Hukumar ta dauki matakin ne bayan karbar rahoton kwamitin binciken korafe-korafen jama’a kan wasu magatakarda guda biyu:

Mustapha Makama na kotun Majistare mai lamba 27; da kuma Yusuf Muhammad Yakasai na kotu mai lamba 14 da ke harabar Kotunan Gyadi gyadi.

“An same su da laifin hadin baki da karbar Naira 130,000 daga wanda ya shigar da korafi cewa za su ba shi belin dan uwansa.”

Sakamakon haka, Hukumar ta umarci Mustapha Makama da yin ritayar dole saboda ba shi da nagarta kuna bai dace ya ci gaba da yin aiki a Ma’aikatar Shari’a ba.

Shi kuma Yusuf Muhammad Yakasai an rage masa matakin girma daya daga matakinsa na yanzu.

Sauran da aka samu da laifi sun ne Salisu Ado Sakataren a Babbar Kotun Jiha da ke Bompai da Bilya Abdullahi magatakarda a Babbar Kotun Jihar Mai lamba 9.

Ake kuma Ismaila Garba da Auwalu Ibrahim Khalil dukkanninsu magatakarda ne da aka samu da laifin hadin baki da cin rashawa ta hanyar bayar da dokar kotu da kwaikwayon sanya hannun jabu na wani akalin kotun Majistare.

“Bayan Kwamitin ya zauna sai ya zartar da shawarar dakatar da su daga aiki.”

Haka kuma Hukumar ta sha alwashin hukunta duk m’aaikacinta da ya yi sakaci da aikinsa, domin ta kare mutunci da kuma rikon amana na tsarin shari’ar don tabbatar da aninicin al’umma.

Shekararu da tawagarsa sun yi watsi da tsarin rabon haraji

An lalata turakun wuta 18 cikin kwanaki 5 a Najeriya — TCN

Sibil Difens ta kama mutum 10 kan aikata laifuka daban-daban a Gombe

’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6 a Gombe