An dakatar da Pogba daga tamaula tsawon shekara huɗu
Wani gwaji da aka yi a Agustan bara ya gano sinadarin testosterone mai yawa a jikin Pogba.
An dakatar da ɗan wasan Juventus Paul Pogba daga buga tamaula na tsawon shekara huɗu bisa samunsa da laifin amfani da sinadarai masu ƙara kuzari.
A watan Satumba na bara aka dakatar da tsohon ɗan wasan na Manchester United na wucin-gadi bayan wani gwajin da aka yi ya gano sinadarin testosterone mai yawa a jikinsa.
- Akwai kurakurai a ayyukan Hukumar Hisbah — Abba Gida-Gida
- Kishin kasa ne mafita ga ’yan Nijeriya – Sarkin Hausawan Kwatano
An gwada Pogba ne bayan wasan farko na Juventus a gasar Serie A a ranar 20 ga watan Agusta.
BBC ya ruwaito cewa Pogba zai daukaka ƙara kan hukuncin da hukumar hani da amfani da kwayoyi masu kara kuzari ta Italiya (Nado) ta yanke.
Da yake magana tun lokacin dakatarwar farko, wakilin Pogba, Rafaela Pimenta, ya ce, “Abin da ya tabbatar shi ne Paul Pogba ba zai taba son karya wata doka ba musamman wadda za ta hana shi tamaula ba.”
Da wannan hukuncin, Paul Pogba ba zai iya taka leda ba har sai shekarar 2027, lokacin da zai cika shekaru 33, bayan an tabbatar da cewa hukuncin zai fara aiki ne daga ranar da aka yi masa gwajin farko.