An dakatar da Pogba kan zargin ta’ammali da ƙwayoyi
Za a iya dakatar da Pogba daga tamaula ta tsawon shekaru biyu zuwa hudu.
An dakatar da ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar Juventus, Paul Pogba daga wasa bisa zargin sa da aikata laifin da ya shafi ta’ammali da ƙwaya.
Hukumar yaƙi da amfani da ƙwayoyi a lokacin wasannin motsa jiki ta Italiya ce ta tabbatar da hakan.
Hukumar ta ce gwajin da aka yi wa Pogba ya nuna cewa an samu sanadarin ‘testosterone’ mai yawa a jikinsa, bayan wasan da Juve ta doke Udinese da ƙwallo 3-0, a ranar 20 ga watan Agusta.
Duk da cewa ba a yi amfani da Pogba a wasan ba, amma yana cikin ƴan wasan da aka zaɓa domin yi masu gwajin amfani da ƙwayoyi bayan kammala wasan.
Bayanai sun ce muddin aka tabbatar da laifin, akwai yiwuwar Pogba zai fuskanci hukunci dakatar da shi daga tamaula na tsawon shekaru biyu zuwa hudu.