An dakatar da Rahama Sadau daga wasan Hausa

Kungiyar Masu Fina-Finan Hausa (MOPPAN) ta kori fitacciyar jarumar nan Rahama Sadau saboda wakar da ta yi inda ta rungume wani mawaki. A faifan bidiyon wakar, wacce ita ce ta farko da jarumar ta yi da harshen Turanci, an nunota tana rungume da mawaki “Classiq” sannan tana kwanciya a jikinsa. Shugaban Kungiyar, Muhammad Kabir Maikaba […]

An dakatar da Rahama Sadau daga wasan Hausa
An dakatar da Rahama Sadau daga wasan Hausa

Jaruma Rahama SadauKungiyar Masu Fina-Finan Hausa (MOPPAN) ta kori fitacciyar jarumar nan Rahama Sadau saboda wakar da ta yi inda ta rungume wani mawaki.

A faifan bidiyon wakar, wacce ita ce ta farko da jarumar ta yi da harshen Turanci, an nunota tana rungume da mawaki “Classiq” sannan tana kwanciya a jikinsa.

Shugaban Kungiyar, Muhammad Kabir Maikaba ya ce an dade ana muhawara kan irin hukuncin da ya kamata a dauka a kan ‘yar wasan. “Sau uku ke nan Rahama na aikata irin wannan danyen aiki, a inda a wannan karon har sai da aka yi kuri’a kuma masu son a kore ta suka yi rinjaye,” inji shi.

Ya ce Rahama da sauran ‘yan mata irinta suna matukar zubar wa kungiyar mutunci a idanun duniya.

Har ila yau, ya ce hakan ne ya sa kungiyar yanke shawarar korar ‘yar fim din domin ya zamo izna ga masu ra’ayi irin nata.