An dakatar da Rahama Sadau wata shida dalilin cin zarafin Zango
Kwamitin Ladaftarwa da ke karkashin kungiyar ’yan fim MOPPAN ta dakatar da jaruma Rahama Sadau tsawon wata shida sakamakon samunta da laifin cin zarafin jarumi Adam A Zango. Kwamatin ya dakatar da jarumar ne shekaranjiya Laraba bayan ya fitar da takardar dakatarwar, sannan ya rarraba ta ga ’yan jarida ciki har da wakilin Aminiya.Kwamitin mai […]
Kwamitin Ladaftarwa da ke karkashin kungiyar ’yan fim MOPPAN ta dakatar da jaruma Rahama Sadau tsawon wata shida sakamakon samunta da laifin cin zarafin jarumi Adam A Zango.
Kwamatin ya dakatar da jarumar ne shekaranjiya Laraba bayan ya fitar da takardar dakatarwar, sannan ya rarraba ta ga ’yan jarida ciki har da wakilin Aminiya.
Kwamitin mai mutum 7 karkashin jagorancin Kamilu Muhammad da mataimakinsa Salisu Mohammed Ofisa da Sakatare Ahmad Alkanawy da mambobin da suka hada da Isma’il Na’Abba Afakallah da Falalu dorayi ya yi zama a ranar Talata da kuma Laraba, inda ya gayyaci Rahama Sadau da kuma Ali Artwork kan zargin jarumar ta ci zarafin Adam A Zango, shi kuma Ali Artwork ya bata sunan Ali Nuhu.
Kwamitin ya bayyana ya samu jarumar da laifin cin zarafin Zango a shafin Istagram dinta, inda aka dakatar da ita tsawon wata shida, shi ma Ali Artwork kwamitin ya same shi da laifin cin zarafin Ali Nuhu, amma kasancewar wannan ne karo na farko da aka taba samunsa da aikata laifi a masana’antar fina-finai ta Kannywood sai kwamitin ya gargade shi, sannan ya rubuta takarda bada hakuri ga Ali Nuhu, ya kuma dauki alkawarin ba zai sake aikata laifi makamancin haka ba. Kwamitin ya gargadi Artwork ne bayan ya yi bincike a kansa, inda ya gano ba mai rigima ba ne
daya daga cikin mamban kwamitin Isma’il NaAbba Afakallah ya ce sun kalli abubuwa biyu ne wajen yanke hukuncin, “jarumar ta tabbatar da ta cin zarafin jarumin a Istagram, amma ta koma ta ba shi hakuri, wanda da ma kwamitinmu ya taba zama a kan ta, lokacin da ta yi rikici da marigayi darakta AGM Bashir, ta rubuta takarda bada hakuri a ranar 23 ga Nuwamba, 2014 da kuma alkawarin ba za ta sake aikata hakan ba. Abu kamar zai ragu sai ga shi ya karu, daga nan muka ce ya zama dole a yi tufkar hanci shi ne muka dakatar da ita tsawon wata shida bayan wannan al’amarin ya faru.”
Afakallah ya ce jarumar ta yi korafin cewa kwamitin bai yi mata adalci ba saboda bai gayyaci Adam A Zango da kuma Ali Nuhu ba don a yi komai a lokaci daya, “Sai muka ce mata kin riga kin amsa laifinki, kin kuma bada hakuri, lokacin da kika cin mutuncin mutumin nan bai ce miki komai ba, haka bayan kin bada hakuri bai ce miki komai ba, babu batun a kira shi idan za a tuhume ki, kasancewar bai ce miki komai ba, bai yi sa-in-sa da ke ba.”
Afakallah ya ce sun dauki wannan matakin ne don tabbatar da doka da oda a masana’antar fina-finai ta Kannywood, ba za su yarda wadansu su lalata Kannywood ba.
Duk yunkurin da wakilin Aminiya ya yi wajen jin ta bakin jarumar abin ya ci tura, inda ta ki amsa kiran wayarsa, ta ki kuma amsa sakon da ya tura mata.