An dakatar da Rasha daga kungiyar kasashe 8 masu arzikin masana’antu
Shugabannin kasashe bakwai masu karfin masana’antu na duniya(G8) sun yi wani taro a birnin Hague na kasar Netherlands inda su kai watsi da tsohon tsarin kunkiyar da ya kunshi kasashe takwas ciki har da Rasha, kuma suka bayyana sabon tsarin da ya kunshi kasashe bakwai(G7) hakan na nufin an cire Rasha daga cikin kunkiyar.Wannan taron […]

Shugabannin kasashe bakwai masu karfin masana’antu na duniya(G8) sun yi wani taro a birnin Hague na kasar Netherlands inda su kai watsi da tsohon tsarin kunkiyar da ya kunshi kasashe takwas ciki har da Rasha, kuma suka bayyana sabon tsarin da ya kunshi kasashe bakwai(G7) hakan na nufin an cire Rasha daga cikin kunkiyar.
Wannan taron ya zo ne ba shiri, a dai-dai lokacin da ake ci gaba da daukar matakan ladaftarwa kan Rasha saboda yadda da ta taimaka wajen ballewar yankin Crimea daga kasar Ukraine. Hakazalika, dakatar da Rasha daga kungiyar ta (G8) wani karin matakin ladaftarwa ne da zai kara mayar da ita saniyar ware. Har-ila-yau an karbe wa Rasha damar ta na bakuncin taron karo na 40 da za a yi a watan Juni mai zuwa, inda aka sauya ta da kasar Belgium.
kungiyar kasashen ta (G7) ta kuma gargadi Rasha kan aniyarta ta yin kutse a kudanci da ma gabacin kasar Ukraine da kuma duk wani abu da zai kawo tashin hankali a yankin, gargadin na nufin idan ta kuskura tai kunnen-kashi za ta fuskanci karin takunkumi mai tsauri.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa taron ya kuma amince Ministocin Makamashin kasashen Turai da su hada hannunsu guri guda don ganin kasashensu sun rage dogaro da kasar Rasha kan bukatarsu ta man fetur da ma ta iskar gas.
A karshe sun umarci Hukumar Bada Lamuni ta Duniya (IMF) da ta shirya tsaf don samar da isassun kudaden da za ta ceto tattalin arzikin kasar Ukraine cikin gaggawa.