An dakatar da shugaban APC a Jigawa kan zargin yi wa ’yar aikin gidansa fyade

Ana zarginsa da yi wa yarinyar ‘yar shekara 14 ne fyaden

An dakatar da shugaban APC a Jigawa kan zargin yi wa ’yar aikin gidansa fyade

Jam’iyyar APC a Jihar Jigawa ta dakatar da shugabanta na Karamar Hukumar Roni, Alhaji Saleh Idris, wanda aka kama bisa zarginsa da yi wa ‘yar aikin gidansa mai shekara 14 fyade.

Dakatarwar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban jam’iyyar a Jihar, Aminu Sani Gumel ya raba wa manema labarai a ranar Alhamis.

A cewar sanarwar, zarge-zargen da ake yi wa dakataccen shugaban sun saba da tanade-tanaden sassa na 21.2 (Vii) da kuma (X) na kundin mulkin jam’iyyar APC na shekara ta 2022 da aka yi wa gyaran fuska.

Sanarwar ta kuma umarci Alhaji Sale da ya mika ragamar shugabancin jam’iyyar a yankin domin ya samu lokacin fuskantar shari’ar da ke gaban shi.

Jami’an hukumar tsaro ta NSCDC ne dai suka kama dakataccen shugaban mai shekara 56, kan zargin lalata da yarinyar wacce ’yar aiki ce a gidan shi.

A cewar NSCDC, an wanda ake zargin ne a ranar Laraba bayan dan uwan yarinyar da aka yi wa fyaden ya kai musu kara kan batun.

“Wani dan uwan yarinyar ne ya kai kara ofishinmu na Karamar Hukumar Roni, bayan wanda ake zargin ya ki amincewa da cikin, inda a maimakon haka ya bukaci su zubar da cikin,” kamar yadda NSCDC ta fada a cikin wata sanarwa.