An dakatar da shugaban jam’iyyar APC da Kwamishina a Kebbi
An zargi shugabannin da ƙin bin ƙa’idojin jam’iyyar.
Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi ta dakatar da shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Abubakar Muhammad Kana Zuru, da kuma shugaban APC na Ƙaramar Hukumar Zuru, Aliyu Abubakar Abiola.
Sakataren jam’iyyar na jihar, Sa’idu Muhammad Kimba, ya ce an ɗauki matakin ne bayan koke-koken da wasu masu ruwa da tsaki daga Zuru suka gabatar kan yadda ake tafiyar da harkokin jam’iyyar.
- Likitoci sun dakatar da yajin aiki bayan alƙawarin biyan haƙƙoƙinsu a Ogun
- Ana siyan fetur da tsada a Najeriya duk da faɗuwar farashin ɗanyen mai
A cewarsa, an zargi shugabannin da sakaci wajen gudanar da ayyukan jam’iyyar, rashin tuntuɓar masu ruwa da tsaki, da kuma ƙin bin ƙa’idojin jam’iyyar.
Ya ce binciken da jam’iyyar ta gudanar ya tabbatar da zarge-zargen da ake musu, wanda hakan ya sa aka ɗauki matakin ladabtarwa a kansu.
Haka kuma, gwamnatin jihar ta dakatar da Kwamishinan Raya Kiwon Kifi, Alhaji Kabir Usman Alaramma.
A wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Yakubu Bala Tafida, ya fitar, ya ce dakatarwar ta fara aiki nan take.
Ya kuma umarci Kwamishinan da ya miƙa dukkanin kadarorin gwamnati da ke hannunsa tare da ayyukan ofishinsa ga babban sakataren ma’aikatar har zuwa wani lokaci.
Har yanzu gwamnatin jihar ba ta bayyana ko dakatarwar Kwamishinan na da alaƙa da matakin da APC ta ɗauka ba.
Sai dai masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin akwai saɓani tsakanin wasu shugabannin jam’iyyar APC a Jihar Kebbi.