An dakatar da shugaban karamar hukuma a Ribas
Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta dakatar da Shugaban karamar Hukumar Ogba/Egbema/Ndoni, Mista Augustine Ahiamadu da kansilolinsa har illa masha Allahu.A wani zama da majalisar ta yi a ranar Talatar da ta gabata, karkashin shugabanta, Adams Dima, majalisar ta bayyana cewa “barnar ta isa haka.” “Dalilan da suka sanya majalisar daukar matakin sun hada da zargin […]
Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta dakatar da Shugaban karamar Hukumar Ogba/Egbema/Ndoni, Mista Augustine Ahiamadu da kansilolinsa har illa masha Allahu.A wani zama da majalisar ta yi a ranar Talatar da ta gabata, karkashin shugabanta, Adams Dima, majalisar ta bayyana cewa “barnar ta isa haka.”
“Dalilan da suka sanya majalisar daukar matakin sun hada da zargin cewa, tun daga lokacin da aka dawo mulkin siyasa, har aka yi zabe, har yanzu wannan karamar hukuma ba zaman lafiya, daga kashe-kashen jama’a sai fadan kungiyoyin asiri, lamarin da ya ki ci ya ki cinyewa,” inji shugaban majalisar.
Yanzu haka majalisar ta nada kwamitin riko da zai jagoranci tafiyar da al’amuran mulki a karamar hukumar inda ta nada Issac Umejuru da Misis Stella Amadi a matsayin shugaba da mataimaki da Augustine Nnadibia da Orji Ebgerikaa matsayin mambobi.
Wata majiyar majalisar da ta nemi a sakaye sunanta ta shaida wa Aminiya cewa Gwamnan Jihar, Nyesom Wike ne ya bukaci a yi hakan sakamakon tashin hankalin da ya yi yawa a karamar hukumar. A karshen watan jiya ma sai da wasu ’yan kungiyar asiri suka tafka wani kazamin fada a karamar hukumar ta Ogba/Egbema/Ndoni.