An dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Lafia

Jatau ya ce matakin ya zama dole domin ba da damar gudanar da bincike kan yadda ake tafiyar da mulkin karamar hukumar

An dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Lafia

Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa

Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Lafia, Mohammed Haliru Arabo, na tsawon wata uku, kan rikicin shugabanci.

Shugaban Majalisar, Danladi Jatau, ne ya sanar da hakan a ranar Talata a Lafia, bayan Shugaban Kwamitin Majalisar kan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu, Musa Ibrahim Abubakar, ya gabatar da korafi kan rikicin mulki da ke faruwa a karamar hukumar.

Jatau ya ce matakin ya zama dole domin ba da damar gudanar da bincike kan yadda ake tafiyar da mulkin karamar hukumar, wanda ya ce yana shafar zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Ya bayyana cewa dakatarwar ta yi daidai da sashe na 7 da na 128 na kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima, wanda ya ba majalisa ikon sanya ido kan harkokin mulki.

A cewarsa: “Domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Lafia, dole ne mu gudanar da bincike kan abin da ke faruwa. Bisa ikon da kundin tsarin mulki ya ba mu, shugaban karamar hukumar Lafia ya dakata na tsawon wata uku. Za a ci gaba da gudanar da harkokin karamar hukumar har sai an kammala bincike.”

Kwamitin harkokin kananan hukumomi da masarautu ya samu umarni da ya gudanar da binciken cikin wannan lokaci. A yayin dakatarwar, mataimakin shugaban karamar hukumar, Uba Arikya, zai rike ragamar mulki.

Tun da farko, Musa Ibrahim Abubakar ya gabatar da kudiri a matsayin gaggawa, inda ya nuna damuwa kan yadda aka dakatar da shugaban karamar hukumar na tsawon wata shida ba tare da bin ka’ida ba. Ya ce hakan ya saba wa kundin tsarin mulki, kuma yana haifar da rashin tabbas a siyasar yankin.

Ya jaddada bukatar majalisar jihar ta shiga tsakani domin tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin kudi da mulkin karamar hukumar.

Kwamitin ya kuma bukaci majalisar ta yi nazari sosai kan lamarin domin kawo karshen rashin tabbas da rikicin da ya kunno kai a Lafia.