An dakatar da Shugaban ’Yan Sanda don satar jarrabawa

A ranar Talatar da ta gabata ne aka dakatar da Sufeto Janar din ’Yan Sandan kasar Indiya har illah ma sha Allahu bayan zarginsa da laifin satar jarrabawa. Ministan Harkokin Cikin Gidan kasar Ramesh Chennitala ne ya ce Sufeton mai suna, TJ Jose ana zarginsa satar jarrabawa saboda duba wasu shafukan wani littafi da ya […]

An dakatar da Shugaban ’Yan Sanda don satar jarrabawa
An dakatar da Shugaban ’Yan Sanda don satar jarrabawa

A ranar Talatar da ta gabata ne aka dakatar da Sufeto Janar din ’Yan Sandan kasar Indiya har illah ma sha Allahu bayan zarginsa da laifin satar jarrabawa.

Ministan Harkokin Cikin Gidan kasar Ramesh Chennitala ne ya ce Sufeton mai suna, TJ Jose ana zarginsa satar jarrabawa saboda duba wasu shafukan wani littafi da ya yi lokacin wata jarrabawar da ya rubuta ranar Litinin da ta gabata, inda daga nan aka sallame shi daga dakin jarrabawar. Kodayake, TJ ya musanta zargin, inda ya ce bi-ta da kulle ne.
Ministan ya ce za a ci gaba da binken abin da ya kira “abin kunya” ga ’yan sanda da kasar baki daya.
Kamar yadda wani rahoto ya bayyana, a watan Maris din da ya wuce, an kama fiye da mutane dubu daya a Jihar Bihar bisa laifin magudin jarrabawa. Har ila yau, duka a cikin watan an samu mutane 300 galibinsu iyayen yara da laifin taimaka wa ’ya’yansu da takardun satar jarrabawa.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta