An dakatar da wasannin Firimiya saboda mutuwar Sarauniyar Ingila

Ta shafe shekaru aru-aru tana hidimta wa kasar mu.

An dakatar da wasannin Firimiya saboda mutuwar Sarauniyar Ingila

Yadda aka karrama marigayiyar yayin wasan da West Ham ta fafata da FC FCSB a gasar Europa ranar Alhamis

Mahukunta gasar Firimiyar Ingila, sun sanar da dakatar da wasannin karshen makon nan sakamakon mutuwar Sarauniyar Ingila, Elizabeth II.

Cikin wata sanarwa da mahukuntan gasar suka fitar a Juma’ar nan, sun ce sun dauki matakin ne domin martaba marigayiyar.

A cewar Richard Masters, babban jami’in Hukumar Kwallon Kafar Ingila ta FA, “mu da kungiyoyin kwallon kafa mun yanke shawarar jingine wasannin karshen wannan mako saboda karamci ga Mai Martaba Sarauniyar Ingila wadda ta shafe shekaru aru-aru tana hidimta wa kasar mu [Birtaniya].

“A matsayinta na Basarakiya mafi dadewa a kan karaga a tarihin Birtaniya, ta zama wata madubi abar dubawa wajen assassa ginshiki da tubali na kyawawan ababen koyo a tsawon rayuwarta.

“A wannan lokaci na juyayi ba ga kasarmu kadai ba hatta ga mililiyoyin mutane a fadin duniya wadanda suke ganin kimarta da karamci, muna tare da duk masu alhinin wannan rashi nata da aka yi.”

Haka kuma, rahotanni sun ce masu kula da gasar tseren doki a Ingila sun sanar da dakatar da ilahirin wasannin gasar sakamakon mutuwar Sarauniyar, a yayin da wasan cricket da za a buga tsakanin Ingila da Afrika ta Kudu shi ma aka dakatar.

Dukkannin wasanni tsere na Juma’ar nan da kuma wasannin Cricket na gasar Heyhoe Flint an soke biyo bayan babban rashin da aka yi a Yammacin ranar Alhamis.

Hakazalika, ba za a yi wasannin kwallon Golf na gasar PGA Championship da ke gudana a wannan Juma’a ba.

Tuni dai shugabannin kasashen duniya sun fara aikewa da sakon ta’aziya ga gwamnatin Birtaniya sakamakon rasuwar Sarauniya Elizabeth ta biyu wadda ta yi shekaru 96 a duniya.

Sarauniya Elizabeth ta rasu bayan shafe shekara 70 a gadon sarauta.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50