An dakatar da yin sallah a wasu masallatai na Saudiyya
Hukumomin kasar Saudiyya sun dakatar da yin sallah a dukkan masallatan kasar, sai dai masallacin Ka’abah da kuma na Madina, kamar yadda kamfanin dillacin labaran kasar ya sanar. A baya dai mahukuntan Saudiyya sun hana masu zuwa aikin Umrah da na Hajji shiga kasar saboda yaduwar cutar kurona. Mutum 133 aka tabbatar sun kamu da […]
Wasu da ke Sallah a masallacin Imam Turki bin Abdullah a Saudiyya. Hoto daga AFB
Hukumomin kasar Saudiyya sun dakatar da yin sallah a dukkan masallatan kasar, sai dai masallacin Ka’abah da kuma na Madina, kamar yadda kamfanin dillacin labaran kasar ya sanar.
A baya dai mahukuntan Saudiyya sun hana masu zuwa aikin Umrah da na Hajji shiga kasar saboda yaduwar cutar kurona.
Mutum 133 aka tabbatar sun kamu da cutar kurona a Saudiyya.
Rahoton BBC