An dambace a Majalisar Dokokin Afirka ta Kudu
An bai wa hammata iska a Majalisar Dokokin Afirka ta Kudu yayin da aka fitar da wasu ‘yan majalisa na daya daga cikin manyan jam’iyyun adawa daga zauran majalisar ta karfi.Suna kokarin kawo rudani ne gabanin wani jawabi da Shugaba Jacob Zuma zai yi shekaranjiya Laraba.Wakilan jam’iyyar Economic Freedom Fighters, sun ce ba su dauke […]

An bai wa hammata iska a Majalisar Dokokin Afirka ta Kudu yayin da aka fitar da wasu ‘yan majalisa na daya daga cikin manyan jam’iyyun adawa daga zauran majalisar ta karfi.
Suna kokarin kawo rudani ne gabanin wani jawabi da Shugaba Jacob Zuma zai yi shekaranjiya Laraba.
Wakilan jam’iyyar Economic Freedom Fighters, sun ce ba su dauke shi a matsayin shugaban kasa ba.
A watan jiya ne Shugaba Zuma ya tsallake kuri’ar tsigewa lokacin da wata kotu ta ce ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar, kamar yadda BBC ta bayyana.
Har ila yau, a ranar Juma’a ne wata babbar kotun kasar ta bukaci a sake fara bincike kan Shugaba Zuma game da zarge-zargen cin hanci da ake yi masa.
A shekarar 2009 ne aka wanke Mista Zuma daga zarge-zargen aikata laifuka 783 wadanda suka danganci cin hanci, lamarin da ya ba shi damar tsayawa takarar shugabancin kasar a wancan lokacin.
Sai dai alkalin babbar kotun Aubrey Ledwaba ya ce wanke shi daga zarge-zargen da aka yi bai dace ba, yana mai bukatar a sake fara gudanar da shari’a kan batun.
Jam’iyyar hamayya ta Democratic Alliance, wacce ita ce ta shigar da kara a wancan lokaci, ta yi maraba da hukuncin kotun.