An damfari wata uwa Naira miliyan 160 a wajen cire wa ’yarta aljani
An damfari wata uwa a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, kimanin Dirham miliyan hudu, wanda ya yi daidai da Naira miliyan 160, don a cire wa ’yarta aljanin da ya hana ta aure. Al’amarin dai ya samo asali ne a lokacin da matar ta shiga damuwa, ganin cewa tsararrakin ’yarta sun yi aure, amma ita ko […]
An damfari wata uwa a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, kimanin Dirham miliyan hudu, wanda ya yi daidai da Naira miliyan 160, don a cire wa ’yarta aljanin da ya hana ta aure. Al’amarin dai ya samo asali ne a lokacin da matar ta shiga damuwa, ganin cewa tsararrakin ’yarta sun yi aure, amma ita ko labari babu.
Da ta shiga tunanin yadda za ta aurar da ’yarta, sai kawar yarinyar ta nuna mata cewa akwai wata amtsala a cikin al’amarin ’yarta, inda ta nuna mata cewa aljani ne ya aure ta. Ita kuwa jin haka, sai ta yarda. Daga nan sai aka nuna mata cewa za a samo mata maganin aljanin da ya hana ’yarta aure. Bayan kwanaki kadan, sai aka bayyana mata cewa aljanin da ya auri ’yarta yana da tsananin kishi, don haka ba zai kyale kowa ya aure ta ba. Kuma shi yake korar duk wanda ya nuna yana son ’yarta.
An dai cusa wa matar ra’ayin ta tuntubi wata bokanya, wadda ta bukaci ta ba Dirhami miliyan guda wato daidai da Naira miliyan 40. Wannan bokanya, sai ta kara da cewa abin wuyanta ma aljani ya kama shi. Don haka aka ce ta bayar da abin wuyan, wanda kimarsa ta kai Dirham dubu 700. Bayan da ta aikata abubuwan da aka bukaci ta yi, sai kuma bokanya ta bukaci ta biya wasu dirhami miliyan biyu da dubu 700, don gudanar da wannan gagarumin aiki na cire aljani. “Jimlar kudin da bokanya ta bukaci a biyata sun kai Dirhami miliyan hudu (Naira miliyan 160),” kamar yadda jaridar Khaleej Times ta ruwaito.
Jaridar Khaleej Times, ta ruwaito cewa, wannan mata ta yi yunkurin sayar da gidanta, don haka ta bayar da cakin kudi na tsawon lokaci, inda za a dauki shekaru har zuwa 20 tana biyan kudin. Sai kawai aka aiko mata da sammaci, wai ana binta bashi. Ganin haka, sai ita ’yarta suka kai kara gaban hukuma, aka kuma bincika, aka gano cewa, matar da ta yi musu wannan kulle-kullen an sha kama ta da laifin damfara.
Hukumar Shari’a ta birnin Abu Dhabi ta bayar da cikakken rahoton wannan badakalar damfara ga jaridar Khaleej Times, inda ta bayyana cewa, tuni matar ta bukaci hukuma ta dakatar da biyan wannan cekin kudin, a kuma soke amfani da shi kacokam.