An damke manomin wiwi a Jihar Jigawa

Hukumat tsaro ta farin kaya (NSDSC) a Jihar Jigawa ta kame wani mai suna Malam Baba Minjili mai shekara 56 a kauyen Sindawa da ke karamar Hukumar Miga da ke jihar, bisa zarginsa da noman tabar wiwi.Shugaban Hukumar NSDSC Malam Muhammed Gidado ya sanar da manema labarai haka a Dutse inda ya ce jami’ansa na […]

An damke manomin wiwi a Jihar Jigawa
An damke manomin wiwi a Jihar Jigawa

Hukumat tsaro ta farin kaya (NSDSC) a Jihar Jigawa ta kame wani mai suna Malam Baba Minjili mai shekara 56 a kauyen Sindawa da ke karamar Hukumar Miga da ke jihar, bisa zarginsa da noman tabar wiwi.
Shugaban Hukumar NSDSC Malam Muhammed Gidado ya sanar da manema labarai haka a Dutse inda ya ce jami’ansa na yi wa wanda ake zargin tambayoyi kafin mika shi gaba. Ya ce ma’aikatansa sun gano gonar tabar ce a tsakiyar wani daji inda ba kowa ne zai iya shiga cikin dadin rai ba. Kwamandan ya ce jami’ansa sun dauki samfurin tabar domin kaiwa dakin gwaji don tantancewa.
Ya ce yanzu haka ma’aikatan leken asiri suna nan sun bazu a yankin don zakulo masu irin wadancan halaye tare da kokarin magance aikata miyagun ayyuka a lungunan jihar.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai wanda ake zargin ya ce yana noman tabar ce domin sayarwa ga masu sha da masu safararta zuwa waje domin samun kudin kula da iyalinsa.