An dasa bom a wajen ɗaurin aure a Borno
Rahotanni sun bayyana cewar an tada bom ɗin ne a wajen ɗaurin aure.
Wani ɗan ƙunar bakin wake, ya hallaka mutane da dama a wajen ɗaurin aure a garin Gwoza da ke Jihar Borno.
Wata majiya ta bayyana cewar mahalarta ɗaurin auren na daga cikin waɗanda abin ya rutsa da su, yayin da wasu da dama suka jikkata.
- Yadda tirelar shanu ta faɗo daga saman gada a Kano
- Matsalar tsaro ta fi tsananta a lokacin Buhari — Shehu Sani
Ya zuwa yanzu babu cikakken bayani game da harin.
An sha kai hare-haren ƙunar baƙin wake a Jihar Borno a lokacin da ake fama da hare-haren Boko Haram, amma jami’an tsaro sun daƙile yawaitar lamarin.
Wata majiyar jami’an tsaro ta shaida wa Aminiya cewa babu tabbas ko bom ne ya tashi a wajen bikin.
“Mun samu tagwayen fashe-fashe; na farko ya faru ne a kusa da Hausari sannan na biyu a kusa da unguwar Mararaba, inda ake sayar da kekuna da kayayyaki,” in ji majiyar.
Rahotanni sun bayyana cewar tuni dakarun sojoji suka yi wa titin garin Gwoza tsinke.
Sai dai ƙwararre kan harkar tada ƙayar baya, ZagaZola Makama, ya ce harin ya faru ne a wajen wata jana’iza.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce: “Wani ɗan ƙunar baƙin wake ya yi basaja a matsayin mai zuwa ta’aziyya, ya tayar da bom a ƙaramar hukumar Gwoza a daidai lokacin da jama’a ke shirin jana’izar waɗanda aka kashe a wani hari.
“Waɗanda abin ya rutsa da su dukkansu fararen hula ne, kuma an taru ne domin yi musu jana’iza.
“Aƙalla ƙarin mutum ɗaya ya rasu yayin da wasu 16 suka jikkata kuma an garzaya da su asibiti. A halin da ake ciki sojoji sun saka dokar hana fita a Gwoza domin daƙile kowace irin barazana.”