An dauke wa kamfanonin da ke kera motoci masu lantarki harajin shekara 10

Sabon tsarin na kamfanonin motoci zai yi aiki ne tsakanin 2023 zuwa 2033.

An dauke wa kamfanonin da ke kera motoci masu lantarki harajin shekara 10

Shugaban hukumar zayyana motoci da tsara su ta Najeriya, Jelani Aliyu

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta fito da sabon tsari da zai yi wa kamfanonin kera motoci da kuma hada su a cikin kasar rangwamen biyan haraji.

Shugaban hukumar zayyana motoci da tsara su ta Najeriya, Jelani Aliyu ya kara tabbatar da wannan ne a bikin baje-kolin motoci da kayayyakinsu na kasashen Yammacin Afirka wanda aka gudanar a Legas inda mataimakinsa, Segun Omisore ya wakilce shi.

A cewar Jelani Aliyu, sabon tsarin yana daga cikin gundarin tsare-tsare da gwamnatin Najeriya ta amince da su game da kera motoci a kasar.

Ya bayyana cewa wannan tsarin ya kunshi yafe wa kamfanonin da ke hada kayayyakin motoci biyan haraji na shekara biyar, sannan kuma gwamnati za ta yafe wa kamfanonin da ke kerawa da hada motoci masu lantarki biyan haraji na shekara 10.

Ya kuma bayyana cewa wannan sabon tsarin na kamfanonin motoci zai yi aiki ne tsakanin 2023 zuwa 2033 kuma babban burin tsarin shi ne samar da kyakkyawan yanayi ga kamfanonin motoci a kasar domin samar da ci-gaba ta bangaren ayyukan da suke yi.

Haka kuma tsarin na da burin kara adadin motocin da ake kerawa a cikin gida da kuma samar da miliyoyin ayyuka.

Duk da cewa akwai kalubale daban-daban da kamfanonin kera motoci ke fusakanta kamar shigar da motocin da aka yi amfani da su cikin kasar ta kan iyaka da kuma tashin dala a kasuwannin duniya, Jelani Aliyu ya tabbatar da cewa za su ci gaba da iyakar kokarinsu domin ganin kamfanonin sun samu nasara.

TRT