An dauke wuta a babban layin lantarki na Najeriya
Karo na biyu ke nan cikin kwanaki hudu ana dauke wuta a babban layin lantarki na kasa, inda a wannan karon wutar ta dauke da misalin karfe 10.50 na safiyar Talata.
Turken wutar lantarki
An dauke wuta daga daya a babban layin wutar lantarki na kasa a Najeriya.
Dauke wutar a safiyar Talata ya sa kamfanonin rarraba wutar lantarki bayar da wutar ya ’yan Najeriya.
Karo na biyu ke nan da hakan ke faruwa a cikin kwana hudu, inda a wannan karon wutar ta dauke da misalin karfe 10.50 na safiya.
Shafin Hukumar Kula da Lantarki ta Kasa (NISO) ta danganta dauke wutar da matsala a layin tura wuta na 330kv da kuma daukewar layukan da ke dauko wuta daga cibiyar tura wuta.