An dauki alwashin yakar masu sayar da magungunan jabu
Hukumar Lura da Ilimin Makiyaya ta kasa (NCNE) tare da hadn gwiwar kamfanin Turner Wright Limited, sun amince su hada karfi da karfe don yakar wadanda suke sayar da magungunan dabbobi na jabu ga Fulani makiyaya. Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da ma’aikatar ta raba wa manema labarai ciki har da jaridar Aminiya […]
Hukumar Lura da Ilimin Makiyaya ta kasa (NCNE) tare da hadn gwiwar kamfanin Turner Wright Limited, sun amince su hada karfi da karfe don yakar wadanda suke sayar da magungunan dabbobi na jabu ga Fulani makiyaya.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da ma’aikatar ta raba wa manema labarai ciki har da jaridar Aminiya a makon, ta hannun mai magana da yawun ma’aikatar mai suna Fidelis Ugochukwu.
Babban-Sakataren Hukumar, Farfesa Rashid Aderinoye wanda Daraktan kula da bin diddig da kididdiga, Malam Ibrahim Yamta ya wakilta; ya bayyana takaicinsa ga yadda wasu ke cutar makiyaya ta hanyar sayar musu da jabu da kuma gurbatattun magungunan dabbobi.
Ya ce, hukumar ta hanyar wani shiri da take gabatarwa a gidan rediyon Tarayya na Kaduna mai taken ‘Don Makiyaya A Ruga’ da kuma kamfe din da take yi na keke-da-keke, NCNE ta wayar da kan makiyaya kan yadda za su yi amfani da magungunan da kuma inda za su samu ingantattun magungunan dabbobi.
Ya bayyana burin hukumar na gabatar da kowane kamfani ga abokanen huldarsa da kuma yadda zai sayar musu da magunguna masu kyau.
Farfesa Aderinoye, ya bayyana cewa ma’aikatar NCNE ta yi tsari don tabbatar da ganin cewa ingantattun magunguna sun isa ga makiyaya sannan kuma ya bukaci kamfanin Turner Wright Limited ya yi amfani da wannan damar don maganin yaudarar da ake yi wa makiyayan.
Da yake jawabi, Manajan Daraktan kamfanin Turner Wright Limited, Dokta Tunde Lawal, ya jaddada aniyar kamfanin na tabbatar da cewa ingantattun magungunan dabbobi sun isa ga makiyaya.
Ya kara bayyana aniyarsa na yin aiki kafada da kafada da ma’aikatar na ceto makiyayan daga bala’in masu sayar da magungunan dabbobi na jabu.